A kwanakin baya bayan nan, manyan 'yan jam’iya da su ka hada da shugaban marasa rinjaye a Majalisar dokoki Hakeem Jeffries da shugaban masu rinjaye a Majalisar dattijai Chuck Schumer sun shaidawa shugaban kasan cewa, da kamar wuya ya yi nasara a zaben na watan Nuwamba, sannan faduwar shi na iya shafar samun nasara a Majalisa.
Shima tsohon Shugaban Amurka Barack Obama, wanda Biden din yayi ma mataimaki na tsawon shekaru takwas, an ruwaito cewa, ya shaidawa abokan siyasa cewa, yuwuwar Biden yayi nasara a zaben na kara kankancewa.
Tun farkon makon nan, dan majalisar dokoki na California Adam Schiff, daya daga cikin manyan masu caccakar Trump kuma na kusa da tsohuwar kakakin Majalisar dokoki Nancy Pelosi wadda har yanzu ke da karfin fada a ji a jam’iyar, ta yi kiran Biden din ya janye da ga takarar.
Schiff ya fada cikin wata sanarwa cewa, idan Trump ya sake dawowa akan shugabancin kasa, to kuwa lallai ginshikin demokradiyya zai raunana, sannan yana da matukar damuwa kan yuwuwar yadda Shugaba Biden zai iya yin nasara akan Donald Trump a watan Nuwamba.