Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyun Adawa A Faransa Na Kokarin Hada Kai Domin Samun Nasara Da Rinjaye A Zaben Kasar


Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron

Jam’iyun adawa na Faransa sun kulla wata yarjejeniya cikin sauri domin kokarin kange nasarar kud da kud ga yar jam’iya mai ra’ayin rikau, Marine Le Pen.

A ranar Talata jam’iyun adawa na Faransa suka kulla wata yarjejeniya cikin sauri domin kokarin kange nasarar kud da kud ga 'yar jam’iya mai ra’ayin rikau, Marine Le Pen a taron gangami na kasa a zagaye na biyu na zaben 'yan Majalisar dokoki, inda da ta ce, jam’iyar ta za ta jagoranci gwamnati ne kawai idan ta samu gagarumar nasara da zama mafi rinjaye, ko kuma kusa da haka.

Babban gangamin na kasa da ya kasance karkashin shugaban jam’iya Jordan Bardella, ya samu mafi rinjayen kuri’u a farkon zagayen zaben 'yan Majalisar dokokin kasar a ranar 30 ga watan Yuni da ya gabata, to sai dai hakan bai ba da nasarar da za a kai ga kafa gwamnatin masu ra’ayin rikau na farko a faransa ba, tun bayan yakin duniya na biyu.

Le Pen ta fada cikin wata hira da kafar yada Labaran Faransa cewa, ba zasu iya amincewa su shiga cikin gwamnati ba idan har ba su yi wani katabus ba. Ta ce hakan zai zama babban cin amanar wadanda suka kada ma su kuri’a. Ta kara da cewa, idan aka ce sun samu kujerun 'yan Majalisar Dokoki 270, to su na bukatar karin wasu kujeru 19, inda a karshe tace, za su je ga sauran abokan tafiya su ji ko akwai wanda ya shirya tafiya tare da su a sabuwar tafiya mai rinjaye.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG