Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Kawancen NATO Sun Kuduri Aniyar Taimaka Wa Ukraine A Yaki Da Rasha


Taron NATO a Washington, 2024.
Taron NATO a Washington, 2024.

Kasashen kungiyar NATO sun caccaki China, Iran, Koriya ta Arewa A Kan mara wa Rasha baya a mamayar da ta ke yi wa Ukraine.

Shugabannin kungiyar tsaro ta NATO sun koma gida ranar Juma’a bayan wani taron kwanaki uku da suka yi a birnin Washington DC, inda suka yi bikin cika shekaru 75 da kafa kungiyar, suka kuma kuduri aniyar tallafa wa Ukraine ta fannin soji zuwa lokaci mai tsawo, sannan sun yi alkawarin cewa makomar Ukraine na a kungiyar NATO. Shugabannin sun kuma caccaki kasashen China, Iran da Koriya ta Arewa saboda yadda suke mara wa Rasha baya a yakin da ta ke yi da Ukraine.

A cikin sanarwar karshen taro da suka fidda, kasashen kawancen sun ce mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine sama da shekaru biyu da suka wuce ta “shafi zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun Atlantika da na Turai, ta kuma kawo cikas sosai ga tsaron kasashen duniya.

Sanarwar ta ayyana Rasha a matsayin kasar da har yanzu ke zaman babbar barazana ga tsaron kasashen kawancen," kasashen NATO sun dauki matakai don tabbatar da cewa Ukraine ta yi nasara a kan Rasha.

Kungiyar ta NATO ta amince da alkawarin ba da taimako ta fanni tsaro ga Ukraine tare da kafa wata sabuwar rundunar soja da ake kira NSATU a takaice, don tsara yadda za a samar da kayan aikin soja da ba da horo ga Ukraine.

A wani taron manema labarai ranar Alhamis, Sakatare-Janar na NATO Jens Stoltenberg, ya ce kungiyar za ta tsara yadda za a samar da gudummuwar ba da horo, da kayan aiki, da sauran tallafe-tallafe ga kokarin da Ukraine ke yi na yaki da mamayar Rasha, ta amfani da cibiyar bayar da horo da ke Wiesbaden a kasar Jamus, da kuma cibiyoyin tsare-tsare a kasashe gabashin Turai.

A wata hira da Sashen Koriya na Muryar Amurka, Tsohuwar Mataimakiyar Sakatare-Janar na kungiyar NATO Rose Gottemoeller, ta ce goyon bayan da aka ba Ukraine zai tura sako mai karfi a kasashen duniya game da mamayar Rasha.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG