Shugaba Buhari wanda ya bayyana wannan kudurin yayin da yake bude babban taron babban hafsan sojin kasar da kuma manyan kwamandojin sojojin daga ko'ina cikin kasar yace tsaro na daya daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa don haka za ayi duk wani abu mai yiwuwa don inganta sashin.
Shugaban wanda Babban Hafsan rundunar Tsaron Kasar, Janaral Lucky Irabor ya wakilce shi yace yanzu haka suna magana da wasu manyan kasashen duniya kawayen Najeriya don samar da makamai masu kwari kuma ingatattu don baiwa dakarun kyakkyawan yanayin murkushe duk wani tsageranci da ta'addanci a kasar.
Shugaban Najeriyar yace tuni wasu kayayyakin yakin suka iso Najeriya kuma ba da jimawa ba sauran zasu iso kasar. Ya jadadawa sojojin muhimmancin aiki tare da kuma musaya da amfanin sirri a matsayin wani matakin shawo kan kalubalen tsaro.
Tun da farko cikin jawabinsa, babban Hafsan Hafsoshin Mayakan Najeriyar, Laftanar Janar Faruk Yahaya yace wannan shekara ta 2021 ta kasance wacce su ka yi fadi tashi a cikinta duba da karuwar matsalolin tsaro kama daga aika aikar 'yan bindiga dadi masu garkuwa da mutane da ma aika aikar 'yan awaren kabilar Igbo masu neman ballewa daga Najeriya.
Janar yahaya wanda ya sha alwashin kara nunka kokari don shawo kan matsalolin ya kuma ce tsare zaman lafiya kamar yadda ake cewa ya ma fi cin nasara a yaki, kamar yadda suke gani a ayyukansu na yau da kullum.
Za a shafe mako guda ana wannan taro da nufin duba irin rawar da sojojin suka taka cikin wannan shekara wajen yadda suke fuskantar matsalolin tsaro da nufin tsara yadda za a tunkari matsalar a shekara mai kamawa.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5