Ranar Lahadi 25 ga watan Oktoba Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira da a "zauna lafiya" a kasar inda hukumomi ke gwagwarmayar kawo karshen sace-sace da wawason rumbunan adana kayayyakin abinci na gwamnati da wasu ke yi bayan zanga-zangar da aka kwashe makonni biyu ana yi a kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka.
Shugaban na Najeriya ya kara da cewa ya na goyon bayan a bi tsarin binciken shari'a a Lagos don bi wa masu zanga-zangar lumana da suka rasa rayukansu hakkinsu, da jami'an tsaron da aka kashe da kuma wadanda suka yi asarar dukiyarsu a lokutan tashin hankalin, a cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar.
Ya kuma "yi kira ga mutane a duk fadin kasar da su ci gaba da zama lafiya da zama ‘yanuwan juna, a cewar sanarwar.
Mummunan farmakin da aka kai kan masu zanga-zangar lumana a Lagos a makon da ya gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 a cewar kungiyar kare hakkokin jama’a ta Amnesty International, ya janyo suka sosai a kasar da ma kasashen duniya.
An kuma caccaki Shugaba Buhari sosai saboda kin yin magana bayan tashin hankalin.