Gwamnonin Arewan da su ka kira wani taron gaggawa a jihar Kaduna sun ce ba su ji dadin abun da ke faruwa a wasu sassan Najeriya ba. Shugaban kungiyar gwamnonin Arewan kuma gwamnan Plato, Simon Bako Lalong shi ya yi magana a matsayin gwamnonin baki daya.
Yace abinda su ke bukata shi ne masu zanga zangar su jira su ga abinda gwamnati za ta yi a matakin jihohi da kuma gwamnatin tarayya. Ya ce gwamnati ba za ta lamunci yadda wadansu suke fakewa da zanga zangar lumana da matasa su ke yi na neman mafita su tada hankalin al’umma ba.
endsars-shugaba-buhari-ya-yi-jawabin-kwantar-da-hankali
endsars-matasan-arewa-sun-bukaci-gwamnati-ta-kawo-karshen-zanga-zanga
an-fafata-tsakanin-masu-zanga-zangar-endsars-da-yan-kasuwa-a-jos
Gwamnonin Arewan sun yaba da kauracewa zanga-zangar da wadansu matasan Arewa su ka yi sannan kuma su ka ce su na tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Suka kuma bayyana cewa suna tuntubar gwamnonin kudancin kasar tare da jinjinawa gwaman jihar Lagos inda lamarin ya fi muni.
Jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari jiya Alhamis, da taron gwamnonin Arewa da kuma na gwamnonin kudu maso yamma dai sun sa wasu sa ran ganin wannnan zanga-zanga ta lafa a fadin kasar baki daya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana jawabi kan zanga zanga
Sai dai masu kula da lamura sun bayyana damuwa ganin shugaban kasar ya maida hankali kan matakan da ya ce gwamnatinsa ta dauka na yaki da talauci a kasar, a maimakon zanga zangar da ta rikide ta zama tashin hankali a wadansu sassan kasar, da kuma rasa rayukan masu zanga zanga da dama a jihar Ikko sakamakon amfani da karfin soji da jami’an tsaro suka yi kan masu zanga zanga a Lekki, lamarin da ya sa gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya kafa dokar hana fita ta tsawon sa’oi 24 kafin bada umarnin takaita zirga zirga na tsawon kwanaki uku da nufin shawo kan tashin hankalin.
Saurari Cikakken rahoton Isa Lawal Ikara cikin sauti:
Facebook Forum