Shugaba Buhari Na Jagorantar Taron Kwamitin Sulhun Kasar Gambia

GAMBIA: Tawagar Shugaban Najeriya Buhari da Sirleaf

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari na jagorantar taron kwamitin sulhu wanda ke da halartar shugaban kasar Senegal da mataimakin shugaban kasar Saliyo da Tsohon shugaban kasar Ghana da kuma shugabar kasar Laberiya.

Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta damkawa shugaba Buhari alhakin fitar tsare-tsaren da zasu kai ga an mika mulki a kasar Gambia cikin ruwan sanyi. Ana sa ran cewa wannan taro zai tsara hanyoyin da za a bi don tabbatar da cewa ba ayi amfani da karfi ba wajen canjin mulki a kasar ta Gambia.

Kungiyar Afirka ta Yamma da Majalisar Dinkin Duniya sun nuna damuwarsu akan koma bayan da ake fuskanta a kasar Gambia, biyo bayan zaben da aka gudanar inda shugaban kasar Yahya Jammeh, ya amsa cewa ya sha kaye kuma zai mika mulki, amma daga baya ya turje cewa an yi masa magudi don haka zai kalubalanci maganar kuma ba zai mika mulki ga wanda ya lashe zaben Adama Borrow.

Dukkan matakan da ake dauka wanda shugaba Buhari ke jarantar kwamitin, ana ran ganin komai ya dai dai ta kafin 19 ga wannan watan da ake ciki, ranar da ake sa ran za a mika mulki ga farar hula a kasar Gambia.

Mallam Garba Shehu, yace yanzu matsayin shugaba Buhari shine a warware wannan matsalar cikin ruwan sanyi, ba tare da an tsunduma kasar Gambia cikin yaki ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Umar Faruk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Buhari Na Jagorantar Taron Kwamitin Sulhun Kasar Gambia - 4'04"