Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatan Tashoshin Jiragen Ruwan Najeriya Na Kira Ga Gwamnati Ta Bi Umarnin Kotu


LAGOS: Tashar jiragen ruwa dake Legas
LAGOS: Tashar jiragen ruwa dake Legas

Wasu sabbin ma’aikatan hukumar tashoshin jiragen ruwa NPA fiye da 500 da aka horas shekaru goma da suka gabata na kira ga gwamnatin Najeriya tabi umarnin kotu da Majalisar Wakilai ta mayar da su bakin aiki.

Kungiyar ‘dalibai masu samun haro da aiki a hukumar ta tashoshin jiragen ruwa ta Nigerian Port Authority, sunyi kira ga shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da ya sa baki don ganin cewa an ‘dauke su aiki bayan kammala horas da su da akayi shekaru goma da suka gabata.

A wani taron manema labarai da wasu mambobin wannan kungiyar su kayi a jihar Legas, sunyi kira ga shugaban kasa da ya yi amfani da karfin ikonsa wajen mayar da su kan aiki, sakamakon kin tabbatar da musu da aikin bayan kammala horon da suka yi a hukumar tashoshin jiragen ruwa ta ‘kasa.

Kungiyar ta bayyana cewa wani duk da yake wani alkalin kotun tarayya ya bayar da umarni a hukuncin da ya zartar a watan Mayun shekara ta 2013 na hukumar tashoshin jiragen ruwa ta ‘kasa da ta dauke su aiki ba tare da bata lokaci ba, hukumar ta yi fatali da wannan umarni. Haka kuma Majalisar Wakilan Najeriya ita ma tayi zama na musamman kan wannan batu, tare da bata umarnin a dauke su aiki tare da biyansu albashinsu da ya kai kimanin Naira Miliyan biyu ga kowa a watan Mayun shekarar da ta gabata.

A cewar Muktari Gana ‘daya daga cikin ma’aikatan, tun lokacin da suka kammala horo suna jiran a aikasu inda zasu fara aiki aka daina biyansu albashi, hakan yasa suka shiga cikin halin kunci.

Wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin yayi kokarn jin ta bakin shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, Malama Hadiza Bala Usman ya ci tura.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG