Shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Adamawa Kwamrad Dauda Maina, ya furta haka lokacin da ya ke maida martini ga ikirarin sakataren gwamnatin jihar Adamawa Dakta Umar Bindir, na cewar albashin wata daya kacal malaman firamare ke bin gwamnatin jiha lokacin da ya ke magana kan kalaman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a jawabinsa na ranar daya ga watan nan cewa gwamnatocin jihohi ba su da hujjar kasa biyan ma’aikata albashi.
Kungiyar kwadago, inji ta bakin shugaban ta gwamnati ta biya albashi ga ma’aikatan da suke karkashin ta kan kari a shekarar da ta gabata abin da ya rage shine na bashin alawus na kudin hutu na shekara biyu. Yayin da ma’aikatan kananan hukumomi, malaman firamare da jami’an kiwon lafiya mataki na farko ke bin bashin albashi na watanni hudu zuwa biyar.
Baya ga albashin watanni hudu da malaman firamaren jihar Adamawa ke bin gwamnati, rabon a yi wa malaman firamare karin girma tun 2008 da kuma rashin biyansu kudaden alawus na hutun shekara hudu inji shugaban kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Adamawa kwamarad Rodney Nathan.
Da yake magana kan tallafi da gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi a bara don rage hakkokin ma’aikata, shugaban kungiyar masu kabar fansho ta kasa reshen jihar Adamawa Kwamarad Samson Almuru, ya ce sun kai kokansu ga Allah Ubangiji saboda dukkan matakan da suka bi na ganin sun sami biyan bukata ya ci tura.
Wakilinmu Sanusi Adamu ya yi nazarin jawabin na shugaba Mohammadu Buhari da ya ce gwamnatocin jihohi ba su da hujjar kasa biyan ma’aikatansu albashi kalaman da mai yiwuwa yana iya jefa gwamnatoci da kungiyoyin kwadago cikin rudani nan gaba.
Saurari rahotan Sanusi Adamu.