A yau ne ‘yan matan Chibok suka kwashi kwanaki dubu da ‘daya a hannun wadanda suka sace su. Duk da cewa an samu ‘yan mata 24 a hannu yanzu sakamakon yarjejeniya da gwamnatin APC ta shiga da ‘yan kungiyar Boko Haram, ‘yan kungiyar BBOG masu fafutukar ganin an kwato ‘yan matan Chibok sunce zasu ci gaba da gwagwarmaya har sai sunga an kwato sauran ‘yan mata 195.
Kungiyar tace sun fito ne yau domin gayawa gwamnati ta tashi daga barci, domin idan ana ganin an cimma ‘yan kungiyar Boko Haram, akwai mutane sama da Miliyan biyu masu gudun hijira da indan har ba a yi hankali ba to za a iya shiga cikin wata masifa irin wadda ta fi ta Boko Haram.
‘Yan kungiyar BBOG dai sun fara zanga-zangar lumana domin juyayin tsawon lokacin da ‘yan matan Chibok su kayi a hannu, inda jami’an tsaro su kayi musu kawanya wani abu da kakakin kungiyar Dakta Iman Shehu, ya bayyana shi da cewa har yanzu jami’an tsaro basu san abin da ake nufi da dimokaradiya ba, har yanzu suna tunanin irin na mulkin mallaka.
Masu fafutukar dai sunce daga yanzu har zuwa ranar Asabar, kowacce rana zasu taka daga dandalin hadin kai na Unity Fountain har zuwa fadar shugaban kasa ta Aso Rock domin isar da sakonsu ga shugaba Mohammadu Buhari.
Saurari rahotan Medina Dauda.