Shugaban Amurka Joe Biden zai yi balaguro zuwa Angola, tafiyar da za ta bashi damar cika alkawarin da ya dauka na ziyartar nahiyar Afrika a lokacin mulkinsa tare da maida hankali kan wani katafaren aikin shimfida layin jirgin kasa.
Aikin, wanda ake daukar nauyin wani bangare nasa da bashin da Amurka ta bayar, zai hade Jamhuriyar Congo da Zambia da kuma tashar ruwan Angola ta Lobito dake gabar tekun Atlantic, inda za ta samar da hanya mafi hanzari da sauki ta fitar da ma’adinai zuwa kasashen yammacin duniya.
An tsara cewa Biden zai yi wani takaitaccen yada zango a tsibirin Cape’ Verde dake yammacin Afrika da safiyar Litinin tare da ganawa da Firai Minista Ulisses Correia e Silva daga nan kuma sai ya nausa zuwa Angola, a cewar fadar White House.
Zai ziyarci gidan adana kayan tarihin cinikin bayin dake babbar birnin kasar na Luanda yayin ziyarar ta yini 2 tare da yada zango a tashar jiragen ruwan Lobito a ranar Laraba.
Ziyarar tasa za ta cika daya daga jerin alkawuran da ya daukarwa nahiyar Afrika.
Har yanzu dai sauran alkawuran basu cika ba, irinsu samawa Afrika kujerun dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Yayin da balaguron na Biden ke zuwa a dai dai lokacin da wa’adin mulkin ke kawo karshe, akwai yiyuwar Donald Trump ze cigaba da marawa aikin jirgin kasan baya tare da zama aboki na kut da kut ga Angola inda ya koma fadar White House cikin watan Janairu, a cewar wasu jami’ai 2 da suka yi aiki a tsohuwar gwamnatin Trump.