A jiya Litinin Jami’an tsaron basu tabbatar da rahotannin kafafen yada labarai dake cewa shugaban kasar Joe Biden ya yanke shawarar barin Kyiv ta yi amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango da Washington ta bata, don kai hari cikin kasar Rasha. Amma sun ce Rasha ba ta da dalilin yin wani korafi.
Da take amsa tambaya daga Muryar Amurka, mataimakiyar sakatariyar yada labaran hukumar Pentagon Sabrina Singh, ta ce "Abin da ke kara ruruta wutar rikicin shi ne yadda sojojin Koriya ta Arewa suka higa fadan yanzu haka."
Amurka ta yi kiyasin cewa, akwai akalla sojojin Koriya ta Arewa 11,000 da ke shiga yankin Kursk a kudancin Rasha, wanda Ukraine ta kwace a wani harin ba-zata da ta kai a watan Agusta, wanda kuma ta ke rike da su har yanzu.
Singh ya fada jiya Litinin cewa, ‘Muna da yakinin za’a shiga fafatawa da su’’
Mai Magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov yayi kakkausan martani ga matakin Amurka, game da bada umurnin yin amfani da makamai masu cin dogon zango a ranar Litinin, cewa hakan ya bude wata sabuwar kofar rincabewar al’amurra, kuma wani muhimmin sabon yanayi bisa yadda irin rawar da Amurka ke takawa a rikicin.
Peskov yayi ikirarin cewa, kasashen Yammaci dake samar da makamai masu cin dogon zango sun kuma samarwa Kyiv muhimman ababen bukata. Ya kara da cewa, hakan ya samar da gagarumin sauyi ga yanayin shigar su cikin rikicin.
Shugaban Rasha Vladimir Putin dai baice uffan ba a fili, to amma Peskov ya nusantar da 'yan jarida ga wata sanarwar da Putin din ya fitar a watan Satumba, inda yace, barin Ukraine ta kaikaici Rasha zai fadada wutar cikicin.
Putin yace, rikicin zai yi sauyawar mamaki. Yace, hakan na nufin kasashen kungiyar kawance ta NATO—Amurka da kasashen Turai na yaki da Rasha.
Dandalin Mu Tattauna