Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya jagoranci bukin tunawa da ranar zagayowar 'yancin kasar a yau Laraba 3 ga Watan Agusta a Tilabery karo na 62, inda ya yi amfani da wannan dama don karrama wasu fitattun mutane ciki har da wadanda suka bada gudunmowa a yaki da kwararowar hamada da kuma wasu gwamnonin jihohin Najeriya 2 da wasu manyan 'yan kasuwa saboda abin da aka kira gudunmowar da suka Bayar wajen karfafa hulda a tsakanin Najeriya da Nijer.
Cikin yanayin annashuwa da farin ciki ne aka gudanar da shagulgulan ranar samun ‘yancin kai ta 3 ga watan Agusta a karkashin jagorancin shugaba Mohamed Bazoum a Tilabery jihar da ke karbar bakuncin wannan buki a bana inda dubban mutanen da suka fito daga sassa daban daban na wannan kasa suka hallara don karrama wannan rana wace Malan Tahirou Garka, kamar sauran ‘yan Nijar, ke daukarta da mahimmanci.
Ta wani bangare ranar samun ‘yancin kai wani lokaci ne na sake jan damarar kare muhalli. Saboda haka a bana hukumomi suka bullo da shirin yashe tafkuna da illahirin kogin da Allah ya albarkaci wannan kasa da su. kuma kamar yadda yake a al’ada idan ranar ta zagayo a kan gudanar da ayyukan dashen itace.
A wannan karon shugaban kasa ya dasa na sa iccen a barikin jandarmomi dake Tilabery da nufin bada odar gudanar da irin wannan aiki a ko'ina a fadin kasar, wanda hakan zai shafi miliyoyin itace. Kanar Maizama Abdoulaye babban jami’i a ma’aikatar gandun daji ta kasa, ya jaddada muhimmancin dashe dashen itatuwa a wannan ranar, kamar yadda za a ji a sauti.
Shugaban ya kuma karrama wasu mutanen da suka bada kyaukyawan misali a kan aiki da wadanda suka taka rawa wajen kare muhalli cikinsu har da marigayi Alhaji Ibrahim Dan Ankara wanda ya dasa itace kimanin 5000 a mashigar garin Tasawa a shekaru 1970. Wani jikansa ne ya karbi wannan lamba.
Haka kuma gwamnan Zamfara Bello Matawalle da na Jigawa Mohammed Badaru da ‘yan kasuwar da suka hada da Alhaji Abdul Samad Isiyaku Rabiu da Aliko Dan Gote da Ambasada Lawan Kazaure na fadar shugaba Buhari kowanne daga cikinsu ya karbi mafi darajar lambar yabo a Nijer saboda abinda shugaban kasa ya kira babbar gudunmowar da suka bayar wajen karfafa hulda a tsakanin Najeriya da Nijar.
Saurari cikakken rahoton Souleyman Barma:
Your browser doesn’t support HTML5