Zaratan Sojojin Amurka Sun Kashe Osama Bin Laden

Bin Laden

Shugaba Barack Obama yace an kashe dan ta'addar da aka fi nema ruwa a jallo a cikin wani gida a kusa da babban birnin pakistan

Shugaba Barack Obama na Amurka, ya bayar da sanarwar cewa zaratan sojojin Amurka sun kashe dan ta'addar da aka fi nema ruwa a jallo a duniya, watau shugaban kungiyar al-Qa'ida, Osama bin Laden, a lokacin fadan da aka gwabza cikin wani gida jiya lahadi a kasar Pakistan.

Mr. Obama ya bayyana wannan a lokacin wani jawabin da yayi ta telebijin daga fadarsa ta White House a daren lahadin nan.

Wannan al'amari ya faru kusan shekaru 10 a bayan mummunan harin da 'yan al-Qa'ida suka kai kan Amurka a ranar 11 ga watan Satumbar 2001.

Tun daga wancan lokacin dakarun Amurka suke farautar madugun 'yan ta'addar dan kasar Sa'udiyya. An samu Osama bin Laden ne cikin wani gida a Abbotabad dake yankin hazara a dab da lardin Punjab.

A bayan da labari ya bazu na mutuwar Bin Laden, Amurkawa sun fito a dukkan manyan biranen wannan kasa su na murnar hakan.


Mr. Obama yace bin Laden ba shugaban Musulmi ko Musulunci ba ne, mutum ne wanda ya kashe Musulmi da yawa. Shugaban na Amurka yace an gano inda bin Laden ya buya tare da taimakon hukumar leken asirin Pakistan, kuma ya bayar da iznin a kai farmaki kan gidan a bayan da aka yi wata da watanni ana bin sawun labarin inda ya buyar.

Mr. Obama ya bayyana wannan farmaki a kan bin Laden a zaman nasara mafi muhimmanci da aka taba samu a kokarin murkushe kungiyar al-Qa'ida, ya kuma ce duk wani wanda yayi imani da ganin zaman lafiya da mutuncin bil Adama zai yi marhabin da mutuwar madugun na al-Qa'ida.

Shugaban ya ce Osama bin Laden ya gamu da hukumcinsa.