NIAMEY, NIGER - To sai dai matasa na nuna rashin gamsuwa da wannan yunkuri saboda yadda abin ka iya hana masu samin aikin yi.
A yayin ganawar da ta hada shi da shugabanin kungiyoyin kwadagon da ke da hurumin magana da yawun ma’aikata wato CNT CDTN USTN USPT da CGSL a Fadarsa don tattauna matsalolin da suka sanya ma’aikatan kwadago yin barazanar shiga yajin aiki a makon gobe, shugaba Mohamed Bazoum ya sha alwashin biyan wasu bukatun da suka tsayawa ma’aikata a rai.
Sakataren uwar kungiyar kwadago ta CDTN Djibrilla Idrissa ya bayyana wa manema labarai jim kadan bayan kammala wannan zama. Ya ce batun kudaden al’aus-alau’s na ma’aikatan dake shirin shiga ritaya na daga cikin abubuwan da shugaban kasa ya ce ya umurci gwamnati da ministan kudi su gaggauta soma zartar da dokar da ta kayyade tsarin, sannan ya ce ya yi niyyar kara shekarun ritaya daga 60 zuwa shekaru 62.
Haka kuma za a fara biyan kudaden fanso a karshen kowane wata a maimakon watanni uku. Kan batun shigar da ma’aikatan kwantaragi a sahun ma’aikatan dindindin ya ce ba zai yi gaggawar yanke hukunci ba domin abu ne dake bukatar nazari a bisa la’akari da yawan ‘yan kwantaragi a yau.
Shugaban ya kuma ce gwamnati ta amince ta kara albashin SMIG sai dai abu ne da taron majalissar ayyukan kwadago zai kayyade shi.
Tuni matakin karin shekarun ritayar ya fara daukan hankulan jama’a. A ra’ayin wasu tsawaita shekarun ritaya wani abu ne da ka iya shafar makomar matasan da suka kammala karatu suna jiran samun aikin yi. Matashin ma’aikacin gwamnati Nayoussa Djimrao na daga cikin wadanda ba sa goyon bayan karin shekarun ritaya.
To sai dai shugaban kungiyar DHD Afrique Kabirou Issa na mai kare matakin na shugaban kasa. A tunaninsa dama da matasa za su yi amfani da ita domin kara samun gogewa akan aiki.
Wannan dambarwa akan batun karin shekarun ritayar ma’aiaktan Nijar daga 60 zuwa 62 na wakana a wani lokacin da ma’aikatan kwadago a Faransa suka tsunduma yajin aiki don nuna adawa da makamancin wannan mataki da gwamnatin Emmanuel Macron ta kudiri anniyar shimfidawa daga shekaru 62 zuwa 64.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5