Shirin Mika Mulki: Buhari, Gwamnoni Za Su Sake Bayyana Kadarorinsu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo da Ministoci 44 a Majalisar Zartarwa ta tarayya da Gwamnoni 28, za su fara bayyana kadarorinsu kafin ranar 29 ga watan Mayu da wa'adinsu zai kare.

Bayyana Kadarori ga dukkanin masu mukaman gwamnati wajibi ne, kuma Hukumar Da'ar Ma'áikata ta ce a shirye ta ke za ta fara ba su fom domin su bayyana kadarorinsu kafin ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara da wa'adin su zai kare.

Wadanda za su karbi wannan fom din su ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da gwamnoni 28 da ministoci 44 da hadiman su, ‘yan majalisar dokokin kasa da na jihohi, da shugabanin kananan hukumomi kamar yadda aka tsara a kundin tsarin mulkin kasar.

Barista Mainasara Kogo Ibrahim Umar

Masanin kundin tsarin mulkin kasa, Barista Mainasara Umar, ya ce a karkashin sashi na 172 zuwa 209 na kundin tsarin mulki Najeriya ya zama dole ga dukkan ma'aikaci ko da karamin ma'aikaci ne ko kuma babban ma'aikaci, matukar dai kana karban kudi daga baitulmalin gwamnati, to ya zama tilas mutum ya bi wannan umurnin.

Mainasara ya ce ganin cewa ana iya take dokar ya sa aka kafa Kotun hukunta ma'aikata, wacce aka fi sani da CCB ko kuma Code of Conduct Bureau a turanci.

Mainasara ya kara da cewa anan ne ake hukunta duk wanda aka same shi da laifin sabawa dokokin aiki wanda hukumar da'ar ma'aikata ke sa ido akai idan mutum ya saba.

Farfesa Usaman Mohammed

Da yake tsokaci kan tasirin bayyana kadarori a lokacin kama aiki da kuma lokacin da wa’adin aikin zai kare na da amfani ga ma’aikaci da kasar, masanin harkokin siyasa kuma Malami a Jami'a Baze da ke Abuja, Farfesa Usman Mohammed, ya ce wajibi ne ga mutum ya bi umurnin hukumar da'ar ma'aikata kuma yin haka yana da amfani, saboda ya kamata a san abin da mutum ya mallaka kada rai ya yi halinsa a bar iyali da matsala.

Usman ya ce kin bin dokoki irin wannan ya fi faruwa a kasashe masu tasowa, ba a Najeriya kadai ba, amma ya kamata ya zama wa mutane izina wajen gyara tunanin su da halayen su, saboda a gujewa cin hanci da rashawa ko yin sama da fadi da kadarorin gwamnati.

Dr. Faruk Bibi Faruk

Shi kuwa kwararre a fanin zamantakewan dan Adam kuma Malami a Jami'ar Abuja, Dokta Farouk Bibi Farouk, ya ce dokokin da kundin tsarin mulki ya tanadar na bayyana kadarorin mutum a lokacin da zai kama aiki da kuma lokacin da zai bar aikin suna da kyau, sai dai abin dubawa shi ne yadda za a yi a hukunta wanda ya yi wakaci watashi da kudade a inda mutum yayi aiki, su ne ba su da wani tasiri sai in an inganta su.

Bibi ya ce abu ne da ya samo asalin tun zamanin mulkin mallaka, saboda haka yana kira ga mahukunta na kasar da su sake karfafa hukumomi irin su EFCC da ICPC domin tsaftace aikin gwamnati.

Su ma sababbin shugabanni da ke shirin shiga gwamnati za su cika wannan fom din na bayyana kadarorinsu, duk da cewa suna da saura kusan watanni uku kafin a rantsar da su.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

Your browser doesn’t support HTML5

MIKA MULKI: Buhari Da Sauran Masu Rike Da Madafun Iko Za Su Sake Bayyana Kadarorinsu.mp3