Dr Kabiru Mato na Jami'ar Abuja ya yi sharhi akan bayyana kadarorin da shugabannin biyu suka yi da kuma abun da zai haifar wa kasar.
Yace abun da suka yi wata rawa ce ta bajinta saboda kafin su yi hakan ana ta korafi akan cewa sai a zabi mutum yana talaka amma cikin dan lokaci kadan sai ya kudance fiye da yadda aka yi zato.
Kansila da kwamishana da gwamna da dan majalisa da wasu masu rike da mukamai kafin a farga sun azurce, sun rikide sun zama attajirai babu wanda ya kaisu dukiya.Da an kama wani mukami sai a shiga handama da babakere.
Bayyana kadarori bukata ce ta tsarin mulkin dimokradiya domin shugabanni su nunawa jama'a cewa sun zo ne su bautawa al'umma ba wai su azurtar da kansu ba. To sai su fito su bayyana kadarorin da suka mallaka, jama'a su yi shaida saboda idan suka gama zasu sake bayyana abun da suka mallaka domin a san ko sun yi sama da fadi da dukiyar jama'a.
Cika wannan doka da shugabannin suka yi shi ne abun tarihi kuma mai tasiri a yanzu da kuma nan gaba.
A lokacin shugaba Jonathan yi ki ya bayyana kadarorinsa. Ya ki ya yi kuma babu abun da ya faru.
Matakin zai karfafa mutane musamman talakawa.
Salon shugaban kasa da mataimakinsa da suka bullo dashi nan da 'yan kwanaki masu zuwa gwamnonin jihohi zasu bayyana kadarorinsu.
Banda gwamnoni tunda shugaban kasa da mataimakinsa sun bayyana kadarorinsu duk wanda zasu nada minista ko ya rike wani babban mukami sai ya bayyana kadarars.
Ga karin bayani.