Dokar Najeriya ce duk wanda zai rike mukamin gwamnati ya bayyana kadarorinsa a fili domin kasar ta san abun da ya mallaka kafin ya kama aikin kana idan ya gama zai sauka ya sake bayyana kadarorin a ga ban banci.
Duk da dokar, kawo yanzu babu wani shugaban kasar bayan mariygayi Musa 'Ya'addu'a da ya fito fili ya bayyana kadarorinsa sai yanzu da shugaba Muhammad Buhari da mataimakinsa Farfasa Osinbajo suka yi bisa ga abun da doka ta tanada.
A takardun da suka cika suka kuma mikawa hukumar dake kula da harkokin bayyana kadarori shugaba Buhari asusun ajiya daya gareshi tare da Union Bank. Yana da ajiyar kudi nera miliyan talatin. Bashi da ajiya a kasashen waje kuma bai mallaki kamfanoni ba ko ma'aikatu.
Mataimakinsa Farfasa Yemi Osinbajo yana da nera miliyan 94 da dalar Amurka 900,000 dukansu a bankunan Najeriya.
Shugaban kasa Buhari da mataimakinsa suna da gidaje daidai gwargwado, wato biyar ko shida kowanensu kuma ba manya ba ne. Wasu ma ciki biyu garesu wasu kuma gidajen laka ne.
Sanin yadda shugaba Buhari ya tafiyar da rayuwarsa babu mamaki a ce bai mallaki kadarori masu dimbin yawa ba. To ko yaya wasu suka ga lamarin?
Wani Alhaji Garba Abdullahi yace kowa ya san ba wani abu gareshi ba duk da manyan mukaman da ya rike. Tunda ya bayyana yanzu sai a ga inda aka nufa kuma. Haka ma wani Babangida ya maimaita.
Yanzu kallo ya koma kan masu rike da mukamai a kasar kama daga gwamnoni da shugaban majalisar dattawa da na wakilai zuwa daraktoci da ma ministocin da shugaban zai nada nan gaba.
Ga rahoton Babangida Jibrin.