Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, ta kunla yarjejeniya da kasar Morocco, da kuma kungiyar masu sarrafa taki ta Najeriya da nufin ganin an samar da dukkan sinadaran da ake bukata domin hada takin cikin farashi mai sauki domin sayar da shi ga manoma a cikin sauki.
Mr Thomas Echo, shine shugaban kungiyar masu sarrafa taki ta Najriya wadda aka hada wannan yarjejeniya da shi, ya bayyana cewa an kulla yarjejeniyar ne akan cewa kungiyar ta samowa manoma taki mai rahusa.
Shugaban kungiyar ya kara da cewa buhun takin da ake sayarwa Naira dubu goma, wannan sabon shiri na bayar da Takin a kan kudi Naira dubu biyar da dari biyar ne kacal. Kuma takin zai kai ga manoma ne ta hanyar gwamnatocin jihohi da diloli da sauran ‘yan kasuwa, wadanda kamfanin ke basu akan farashin kowane buhu akan kudi Naira dubu biyar su kuma su kara dari biyar.
Manyan ‘yan kasuwar takin sun fara korafin cewa Tsarin yayiwa wadanda jarinsu bai kai ba sarkakiya, kamar yadda Bashir Abdulla, daya daga cikin kananan ‘yan kasuwar ya bayyana cewa sharuddan da aka bada na cewa dole ne dan kasuwa ya fara daga Tirela guda zuwa abinda ya yi sama, sai dai manyan hamshakan ‘yan kasuwa kada.
Ga Isa Lawar Ikara da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5