A yayin da yake zantawa da manema labarai, shugaban kungiyar manoma da masu fataucin albasa ta kasa Aliyu Isah, ya ce masu fataucin albasa daga Arewacin Najeriya zuwa yankin na kudu maso gabas, sun sha fuskantar farmakin ‘yan bindiga a yankin.
Shugaban ya ce wannan yanayi ya sa ba su da wani zabi illa su daina kai albasa, wadda tana daya daga cikin muhimman sinadiran girki a yankin, har sai al’amura sun daidaita.
Ya yi da’awar cewa ko a kwanan nan ma wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar fafutukar kafa kasar Biyafara wato IPOB ne, sun kwace wasu manyan motoci 2 na albasa.
Aliyu Isah ya ce ko baya ga barazanar da membobinsu ke fuskanta na rayuwarsu, haka kuma suna asarar dimbin dukiyoyinsu sakamakon ayukan ‘yan bindigar a yankin.
Karin bayani akan: Ahmed Gulak, Biyafara, IPOB, Nigeria, da Najeriya.
Idan za’a iya tunawa, ko ikirarin da jami’an tsaron Najeriya suka yi na kashe ‘yan bindigar da suka kashe Ahmed Gulak a jihar Imo, sun ce sun same su ne suna rarrabawa mutane wata babbar motar albasa da suka kwace.
Sha’anin matsalar tsaro na kara ta’azzara a yankin na kudu maso gabashin Najeriya, sakamakon ayukan ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne, da kuma rundunar tsaro ta gabashi wato ESN, wadanda suke kai farmaki kan jami’an tsaro da hukumomin gwamnati.