A yayinda ake shirye shiryen gudanar da bikin sallah karama, wasu magidanta da yan kasuwa sun baiyana matsalolin rashin kudi a matsayin abinda ke neman rage karsashin bikin Sallah karamar.
Magidanta da sauran al'ummar Musulmi su koka gameda tsadan kayayyakin masarufi da kuma rashin kudin gudanar da wannan biki kamar yadda aka saba yi a duk shekara.
Wasu magidanta da iyalai da wakilin sashen Hausa a Lagos, Babangida Jibirin ya zanta dasu akan bikin wannan Sallah, sun baiyana ra'ayinsu.
Malam Sulaiman Ibrahim yace a gaskiya basu samu matsalolin sosai ba, sai abinda ba'a rasa ba, saboda yace yan kasuwa sunyi kokari iya nasu, amma akwai wasu yan kayayyaki wadanda farashin su ya sauka, akwai kuma wadanda ake son 'yan kasuwa su taimakawa magidanta su rage farashin su.
Shi kuma wani mutum yace ya bar komai hannun Allah, kodayake ya tanadi abubuwan da yake bukata. Haka kuma ya saya wa 'ya'yan sa kayan Sallah, duk da matsalolin da ake fuskanta.
Bincike ya nuna cewa akwai ma'aikatu da kamfanoni da dama wadanda basu biya ma'aikata albashin wannan wata ba. A wasu jihohin kuma, ma'aikata na binsu basussukan na albashin baya, lamarin daya kara wahalhalun da magidanta ke fuskanta.
Your browser doesn’t support HTML5