Kalubalen tsaro ba wani sabon abu ba ne tun shekarar 2010 da 'yan ta'ada suka tada bam a wurin bukin tunawa da ranar samun 'yancin Najeriya a Abuja
Masanin harkokin tsaro Rabe Nasiru yace aiki na kwarewa ne kawai zai kawo karshen tabarbarewar tsaro. Yace inda ake da hukumomin tsaro iri-iri kuma abubuwa suna faruwa sai a yi mamaki menene suke yi. A wasu wurare tun lokacin da mutum ke shirya ta'adanci hukumomin tsaro zasu bankado shirin su kama mutumin su kuma gurfanar dashi gaban shari'a.
Amma a Najeriya 'yan ta'ada sai su fito su fadi ranar da zasu aikata aikin ta'adanci ya kuma tabbata haka. Tambaya nan ita ce shin gwamnati na bin kwarewa wajan tunkarar kalubalen tsaron. Shirin dakarun gaba basa samun bayanai akan shirin gwamnati na kai masu hari kuwa?
Janar Mansur Dan Ali mai ritaya yayi aiki a kwamitin tsaro na taron kasa da aka gudanar bara. Yace mutane suna yawan katsa landan akan abubuwa da basu sani ba. Yace tsaro ba abu ba ne da kowa zai ce a yi wannan ko wancan ba. Abubuwa ne da ya kamata a barwa kwararru su yi abun da yakamata. Yace wannan na cikin matsalolin da kasar ke fama dasu.
Janar Mansur ya yi ikirarin cewa sabbin manyan jami'an tsaro da shugaba Buhari ya nada zasu kawo banbanci domin da can akwai munafurci a cikin aikin. Dama basa son a kawo karshen rikicin. Yace a cikin wadanda suke rike da harkar tsaro wasu na zarewa su je su tseguntawa 'yan ta'ada shirin da ake yi. Su ne suke bada labaran abubuwan da ake shiryawa domin yakarsu.
Janar Mansur ya ci gaba da cewa yakin sunkuru kamar wanda ake yi da Boko Haram sai an bi bayanan siri bisa ga leken asiri a yi anfani dasu kafin a samu cigaba.
Dangane da sabbin shugabannin jami'an tsaro Janar Mansur yace kwararru ne wadanda suka san abun da suke yi ba kamar na da ba da suke cika mutane da farfaganda, wato suna karya da nufin yaudarar mutane.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya