Lauyan da ke kare tsohon gwamnan Jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na fuskantar tuhuma bayan da bayanai suka nuna cewa ya yi karya a gaban kotu a lokacin da ya je kare tsohon gwamnan.
A ‘yan kwanakin da suka gabata, Lauya Okechukwu Nweze ya nemi kotu ta hana hukumar EFCC mai yaki da yiwa arziki zagon kasa ta kama Kwankwaso.
Kungiyar ‘yan fansho reshen Jahar Kano ce ta shigar da karar tsohon gwamnan bisa zargin cewa ya sarrafa kudadensu ba bisa ka’ida ba.
Yanzu haka kotun ta ba da umurnin kungiyar lauyoyi ta Najeriya da ta ladabtar da lauyan tsohon gwamnan, Nweze.
ABINDA MASANA SHARI’A KE CEWA
Yanzu haka masana shari’a sun fara tofa albarkacin bakinsu game da salon da wannan takaddama ta dauki.
“Wajibi ne kungiyar lauyoyi ta kasa ko kuma ta Jahar Kano, su bincika wannan zargi da ake wa wannan lauya na cewa ya shigar da kara ba tare da iznin tsohon gwamna Kwankwaso ba.” In ji wani masanin shari’a, Barrister Musa Aliyu.
Ya kara da cewa, dokokin sha’anin gudanar da aikin lauya sun nuna cewa wajibi ne duk abinda lauya zai fada a gaban kotu ya kasance gaskiya ya ke fada.
“Idan ya fadi binda ba gaskiya ba ne kuma kotu ta gano haka, to kotu na damar ta janyo hankalin kungiyar lauyoyi ta kasa ko ta jahar da yake na cewa su bincika kuma a dauki mataki a kansa.” Ya jaddada
Sai dai Barrister Aliyu ya ce bai taba gani lauya ya je kotu ya ce yana kare wani ba kuma lamarin ya zo ya kasance ba da yawun wanda ake karewa ba ne.
“Saboda haka idan an ce ya je kotu ba tare da iznin Kwankwaso ba, zan yi mamaki gaskiya, saboda wannan lauya na san lauyan Kwankwaso ne fiye da shekaru goma sha wani abu.” In Ji Aliyu
Ga karin bayani a cikakkiyar hirar da Wakilin Muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari ya yi da Barrister Musa Aliyu: