Dr. Abubakar Umar Kari masanin kimiyar siyasa na Jami'ar Abuja ya bayyanawa Muryar Amurka ma'anar sake fasalin tsarin mulki Najeriya.
Dr. Kari ya ce sake fasalin mulkin kasa na nufin duk wani arziki dake wani yankin kasar bai kamata ya zama na kasar gaba daya ba, na wannan yankin ne.
"Abun da yankin ko lardin zai yi shi ne ya dinga biyan gwamnatin tarayya haraji na abun da ya samu. Kowa ya ci gashin kansa." In ji.
Sai dai 'yan siyasa irinsu Alhaji Aliyu Sale Bagare wanda tsohon mataimakin gwamna ne a jihar Yobe suna da ra'ayi daban, ya ce tsarin da kasar ke kai yanzu baya bukatar wani garambawul.
Yana mai cewa duk wanda yake son a sake tsarin mulkin Najeriya ya isa a kirashi "babban maci amana amanar kasa" domin bai san irin gwagwarmayar da shugabannin farko suka yi ba kafin kasar ta samu 'yanci daga turawan mulkin mallaka.
Ya ci gaba da cewa Allah ne kadai ya san dalilin da ya sa ya dunkule kasar ta zama kasa daya kana ya albarkace ta da mutane da dimbin arzikin mai da ma wasu.
Domin jin cikakken rahoto kan wannan batu, saurari wakilinmu Hassana Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5