Sama da wuta guda bayan da ba a ji duriyarsa ba, wani faifa dauke da muryar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya na gaida Musulmi kan kammala azumin watan Ramadana da suka yi ya janyo muhawara a kasar.
Yayin da wasu ke ikrarin ba muryar B uhari ba ce, wasu kuwa gani su ke bai dace shugaban ya yi magana da harshen Hausa ba lura da cewa da harshen ingilishi kasar ke gudanar da harkokin mulkinta.
Kabiru Dahiru Rahama ya na mai cewa sun ji faifan dauke da muryar da aka ce ta Shugaba Buhari ce, amma su abun dake damun su shi ne sanin zahirin halin da shugaban yake ciki.
Ya kuma zargi wadanda suke kusa da shugaban akan cewa su na yaudarar mutane ne.
Dan jarida Ja'afar Ja'afar ya na ganin bai ma dace a fitar da muryar shugaban kasa a halin yanzu ba.
Ya ce sakon cikin harshen Hausa kadai aka yadashi kuma kasar ta na da harsunan da yawa.
A cewar Ja'afar, yadda shugaban ya yi maganar ya yi kamar an takura masa ne ya fadi sakon.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina domin jin sauran wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu.
Facebook Forum