Wannan lamari dai ya janyo cecekuce a sassa daban daban na kasar har da ma kasashen waje inda Iran ta nemi hukumomin Najeriya su saki shugaban kungiyar ta Shi’a Sheikh El Zakzaky da aka kama.
Rahotanni sun ce a lokacin da ‘yan Shi’a ke gudanar da wani taron su a unguwar Gyellesu da ke Zaria jihar Kaduna ne ayarin motocin shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai, ta zo shigewa, inda aka zargi mabiya Shi’ar da hana su wucewa.
Lamarin wanda ya faru ranar 12 ga watan Disamba ya kai ga takaddama inda aka yi arangama har aka yi zargin sojojin Najeriya sun kashe daruruwan mabiya Shi’ar, suka kuma kai hari a Hussainiya na ‘yan kungiyar.
Bayanai sun nuna cewa sojojin sun yi ta magiya a barsu su wuce amma hakarsu ba ta cimma ruwa, wanda hakan ya sa suka fusata.
An dai kama shugaban kungiyar wanda yake hanu tare da iyalinsa yayin da ake ci gaba da tsare wasu mambobin kungiyar ta ‘yan uwa musulmi tare da rike wasu gawarwakin 'yan kungiyar.
Domin jin karin bayani kan jawabin da gwamna El Rufa’i ya yi da kuma tabbacin da kwamitin ya bayar na yin adalci a binciken musabbabin rikicin bayan da aka rantsar da mambobin kwamitin a ranar juma'ar da ta gabata, saurari rahoton wakilin Muryar Amurka, Lawal Isa Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5