Sakamakon rikice-rikicen da ake samu tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma a kudancin jihar Taraba ta arewa maso gabashin Najeriya, yanzu haka shugabannin Fulani a jihar, sun ce sun dau matakan kawo karshen rigingimun.
Taron Fulanin, wanda aka yi karkashin kungiyar Fulani ta kasa da kasa ta Tabital Puulaku, ya yi zargin cewa da hannun wasu dake amfani da wadannan rikice-rikicen don cimma muradunsu, batun da suka ce a yanzu ba zasu sake amincewa ba.
Shugaban kungiyar a jahar Taraba, Bello Bamme Alhaji Nyame ya jaddada cewa sun hada kai da gwamnatin jahar ne saboda a san cewa ba su tare da wadanda ya ce sun a sato kayan mutane daga wasu jahohi sun a kawowa jahar. Shi ma Sarkin Fulanin Hardo-Kola, Alhaji Ali Jauro ya yi kira ga Fulani da manoma su ki yadda miyagu na hada su fada don amfanar kansu.
Ga wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz da rahoton: