An yi zargin cewa yawan wadanda harin ranar Lahadin da ta gabata ya rutsa da su a kauyen Kho na Karamar Hukumar Gerei da ke jihar Adamawa ya haura sittin da takwas, zargin da makiyaya su ka karyata.
Kungiyar raya yankin na Kho ce ta ba da sabbin alkaluman, lokacin da ‘ya’yanta suka koma kauyen, wanda yanzu haka ya zama tamkar kufai, domin jana’izar ‘yan uwansu da aka kashe a harin.
Shugaban kungiyar, Mr Stephen Ngwasete, ya nuna takaicinsu saboda rashin ba su kariya, duk da cewar sun sanar da hukumomin tsaro barazanar Fulani makiyayya na kai masu harin ramuwar gayya ‘yan kwanaki kamin su kai harin; da kuma rashin kai masu tallafi kwanaki uku bayan aukuwar lamarin.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa, Mallam Mohammed Ghazali, ya ce ba ‘yan Boko Haram ne su ka kai harin ba – makiyaya ne, zargin da sakataren kungiyar Miyyetti Allah reshen jihar Adamawa Mal. Abubakar Nyako ya karyata.
Ga wakilinmu a Adamawa Sanusi Adamu da cikakken rahoton: