Shettima Ya Bar Najeriya Zuwa Kasar Ivory Coast

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima (Hoto: Facebook/Kashim Shettima)

Ana sa ran mataimakin shugaban kasar ya dawo Abuja da yammacin yau Laraba.

Da safiyar yau Laraba, mataimkin shugaban Najeriya Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin Abidjana, na Ivory Coast.

Sanarwar da hadimin shugaban kasa na musamman akan harkokin yada labarai (a ofishin mataimakin shugaban kasa), Stanley Nkwocha ya fitar a yau Laraba, yace Shettima zai halarcin bikin bude taron baje kolin kayayyakin hakar ma’adinai da albarkatun makamashi na duniya (SIREXE) na bana.

Taron na SIREXE wani al’amari ne na kasa da kasa da gwamnatin Ivory Coast ta shirya da ya mayar da hankali kan “manufofi da dabarun samarda cigaba mai dorewa a bangarorin hakar ma’adinai dana makamashi.”

Taron zai gudana ne tsakanin ranaikun 27 ga watan Nuwamban da muke ciki zuwa 2 ga watan Disamba mai kamawa, a cibiyar baje kolin birnin Abidjan.

Ana sa ran mataimakin shugaban kasar ya dawo Abuja da yammacin yau Laraba.