Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, tare da wasu mutane biyu, sun gurfana a gaban kotun babbar tarayya dake Abuja ranar Talata, inda suka musanta zargin aikata laifuffuka 16 da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar musu.
Tsohon gwamnan, wanda yake matsayin wanda ake tuhuma na farko, ya bayyana gaban Mai Shari’a Maryann Anenih, inda ya musanta dukkan zarge-zargen da aka karanta masa a gaban kotu.
Bayan sun kammala karanta tuhume-tuhumen, lauyan wanda ake tuhuma, Joseph Daudu, ya gabatar da bukatar beli ga kotun. Sai dai lauyan EFCC, Kemi Pinheiro, ta kalubalanci wannan bukatar, tana mai cewa belin wanda ake tuhuma na farko ya kare tun watan Oktoba.
Da yake martani, lauyan wanda ake tuhuma ya ce akwai sabuwar takardar neman beli da suka gabatar ranar 22 ga Nuwamba, inda ya dogara da dukkan bayanan da aka tattara a cikin takardar rantsuwar neman beli. Ya kuma nuna cewa wanda ake tuhuma ya girmama doka, kasancewar ya bayyana a kotu kamar yadda aka bukata.
Lauyan EFCC ta nemi a fara shari’ar nan take, tana mai cewa hukumar ta shirya gabatar da shaidarta ta farko. Amma lauyan Bello ya nemi lokaci domin ya yi shiri, yana mai cewa an mika masa tuhume-tuhumen ne da tsakar daren ranar 26 ga Nuwamba.
A yayin gabatar da hujjoji kan neman beli, lauyan Bello ya jaddada cewa, doka a Najeriya tana ganin wanda ake tuhuma a matsayin mara laifi har sai an tabbatar da akasin haka. Ya kuma bayyana cewa a cikin dokar kasa, wanda ake tuhuma na da ’yancin yin shiri cikin ’yanci yayin da ake jiran ci gaban shari’a.
Sai dai lauyan EFCC ta kalubalanci wannan matsaya, tana mai cewa wasu daga cikin batutuwan da aka gabatar a matsayin hujja sun shafi wata shari’a daban da ake yi a Kotun Tarayya.
Daga karshe, kotun ta saurari bangarorin biyu kuma ta dage zaman domin yanke hukunci kan bukatar beli da kuma ci gaba da sauraron shari’ar. Wannan na zuwa ne bayan an bayyana cewa sauran wadanda ake tuhuma, Umar Shoaib Oricha da Abdulsalami Hudu, sun samu beli.
Zaman kotun ya ja hankalin jama’a, inda ake ci gaba da bibiyar wannan lamari mai daukar hankali a siyasar Najeriya.
~Yusuf Aminu Yusuf
Dandalin Mu Tattauna