Shekaru 16: Ra’ayoyin Jama’a Akan PDP

Godsday Orubebe daga PDP.

Za’a iya cewa tun daga Janhuriya ta farko har zuwa ta hudu mai shudewa, jam’iyyar PDP tafi kowace jam’iyya rike mulki a Najeriya, bayan kwashe shekaru 16 tana shugabanci babu kakkautawa.

Wasu daga cikin mazauna birnin Tarayya Abuja, sun bayyanawa Muryar Amurka abubuwan da baza su manta ba a shugabancin PDP.

Aisha Abdullahi daga birnin Maiduguri cewa tayi “bai wai bai yi abun a zo a gani ba, gaskiya abun da yayi, don harkokin da yayi na rashin kyau din na PDP yafi abubuwa masu kyau yawa.”

Shi kuwa Bashar Babandi Gumel cewa yayi “abun dai shine, rasa wasu daga cikin abokai, wadanda suke ‘ya’yan wannan jam’iyya tunda duk inda bawa yake, baya rasa wadansu abokai da yake muamala da su, a wadansu al-amura na rayuwa ko mene ne.”

Ga Maryam Bagudu:

“To a mulkin dai da PDP tayi, gaskiya zamu ce babu laifi sun da taka rawar gani. Domin kamar ni dai mun samu a cikin gidajen da shugaban kasa ya kaddamar, da yadar Allah mun samu”.

Wannan shine karo na farko da shugaba wanda aka zaba a siyasance ya mika mulki ga wani wanda ba dan jam’iyyarsa ba. Shugabancin Goodluck Jonathan ya fuskanci kalubale sosai, musamman ma matsalar tsaro wanda ya raba jama’a da yawa da rayukansu, da kuma arzukansu.

Your browser doesn’t support HTML5

Shekaru 16: Ra’ayoyin Jama’a Akan Shugabancin PDP - 2'03"