Adamu Maina Waziri sakataren garanbawul din jam'iyyar PDP yace shugaba Jonathan ya matsawa Alhaji Ahmadu Mu'azu ya bar shugabancin jam'iyyar.
Maina Waziri yace jam'iyyar PDP ta shiga halin da ta tsinci kanta ba domin kowa ba saboda Shugaba Jonathan ne. Shi ne limamin umalubaisan masifar da ta addabi jam'iyyar har ta kaita da yin asarar gwamnoni da 'yan majalisu da ma gwamnatin tarayya gaba daya.
Yace abun da ma ya faru rahama ce ta Ubangiji domin barnar da shugaba Jonathan ya yiwa kasar da kasar ta wargaje ne gaba daya.
Yace shi Jonathan ya tashi baya son Ahmadu Mu'azu ba domin komi ba domin Ahmadu Mu'azu ya ki yadda da bukatarshi. Bayan ya fadawa duniya da bakinsa cewa ya sha kaye sai ya bukaci Ahmadu ya kai karar rashin amincewa da sakamakon zaben.
Ahmadu a matsayinsa na shugaban jam'iyya yace ba zai yi hakan ba domin shugaban kasa ya riga ya amince ya sha yake. Saboda haka yace shi ba zai kai kara kotu ba. Wannan lamarin ya kara dagulawa jam'iyyar harkokinta.
Daga ranar 29 ga wannan watan dole jam'iyyar ta fuskanci gaskiya cewa ta fadi amma kuma ta fitar da sabon shugaba wanda dole ne ya fito daga yankin arewa maso yamma.
Banda murabus din shugaban jam'iyyar Alhaji Ahmadu Mu'azu, shugaban kwamitin amintattu Tony Anenih shi ma ya yi murabus. Yanzu Sanata Walid Jibril ya maye gurbinsa a matsayin mukaddashi.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.