Jam’iyyar PDP mai shirin barin gado a Najeriya ta ce murabus din da shugaban ta Alhaji Ahmed Mu’azu ya yi ya zo a makare.
Jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar shiyyar areaw amaso gabashin Najeriya, Alhaji Al- Amin Sani Muhammad ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da wakilun Muryar Amurka.
“Dalilin da ya san a fadi haka shi ne, akwai maganganu da aka yi ta yi bayan faduwar zabe, wanda aka ce shi tsohon shugaban jam’iyya ya fadi cewa idan ya bar shugabancin ja’iyyar nan ko za ta tarwatse ne ko za ta wargaje ne, wani abu mai kama da haka.”
Da ka tambayi Alhaji Sani ko ajiye aikin na Ahmed Mu’azu ya rage musu kwarin gwiwa, sai ya ce “to yanzu jam’iyya za ta tashi ta baiwa wanda ya dace shugabancin jam’iyyar, wanda zai mayar mata da kimar ta.”
Tuni dai ‘yan Najeriya su ka yi ta tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan lamari inda wasu ke cewa hakan da ya yi hi ne dai dai.
“Abin da ya kamata ya yi ke nan, saboda ya jefar da kwallon mangwaro ya huta da kuda.” In ji Hajiya Hadizan Babuji, wata mazauniyar garin Bauchi.
A jiya ne dai Ahmed Mu’azu ya mika takardar ajiye aikin nasa fiye da wata guda bayan da jam’iyyar ta PDP ta sha kayi a zaben da aka gudanar.
Ga karin bayani a hirar wakilin Muryar Amurka da Alhaji Al Amin Sani Muhammad: