Adamu Maina Waziri wanda jigo ne a jam’iyyar ta PDP ya ce ya kamata a ce an sanarwa da mutane cewa shugaba mai jiran gado zai yi “bulaguro.”
“A zance na shugabanci, abin da ya kamata a yi shi ne, ya kamata a ce an fadawa jama’a sabon shugaba zai yi bulaguro don wasu uzuri na son kanshi ba kawai mutane su je masallaci su yi tsammanin za su ganshi sai su je ba su ganshi ba.”
Bayanai na cewa a jiya juma’a ne Buhari ya fice daga Najeriyar zuwa Burtaniya domin yin hutun karshen mako, a dai dai lokaci da aka shirya wani taron addu’a domin neman gwamnatinsa ta fara a sa’a.
Game da batun hamayyara da jam'iyyar PDP za ta yi, Waziri ya kara da cewa daga ranar da aka rantsar da Buhari za su fara mai shari’a akan abubuwan da ya fada cewa zai yi a kasar, musamman abin da ya shafi tsaro.
“Na farko tsaro ke nan, na biyu magance cin hanci da rashawa a Najeriya na uku rashin adalci da ya addabi kasar nan, saboda haka wadannan abubuwa guda uku idan ya fara da su, sune kiran sallarsa da ya kamata ya fara da su.”
Ya kara da cewa “saboda haka ba za mu bata lokaci ba, daga ranar farko za mu fara yi mai shari’a akan abubuwan da muke tsammanin zai yi mana, idan bai mana ba kuma za mu fada cewa bai yi ba.” Inji Waziri.