An yi bikin tunawa da marigayi Patrick Ibrahim Yakowa gwamnan jahar Kaduna da ya rasu bara a hatsarin jirgin sama a Najeriya
WASHINGTON, DC —
Wakilin Sashen Hausa a Kaduna Isah Lawal Ikara ya halarci bikin da aka yi don tunawa da gwamnan jahar marigayi Patrick Ibrahim Yakowa wanda Allah Ya yiwa rasuwa ranar goma sha biyar ga watan Disamban shekarar dubu biyu da goma sha biyu cikin wani hatsarin jirgin saman da ya faru a jahar Bayelsa. An yi bikin ne albarkacin cikon shekara daya da mutuwar gwamnan marigayi. Isah Lawal Ikara ya tattauna da uwargidan marigayin Mrs.Amina Ibrahim Yakowa wadda ta kara yiwa Allah godiya, kuma ta kara yabon marigayin wanda ta ce shekarun su talatin da hudu su na zaman aure kamar yadda za ku ji a cikin rahoton da ya aiko daga Kaduna:
Your browser doesn’t support HTML5