A ranar Juma’a 9 ga watan Afrilun 1999 ne General Ibrahim Ba’are Mainassara ya hadu da ajalinsa bayan da wasu sojoji masu tsaron lafiyarsa suka bude masa wuta a filin jirgin saman Escadrille a wani lokacin da ake cikin yanayin ce-ce-ku-cen siyasa inda ‘yan adawa na wancan lokaci suka yi watsi da sakamakon zaben da ya ayyana shi a matasyin wanda ya yi nasara.
Shekara 22 bayan wannan kisa har yanzu shiru ake ji akan maganar binciken da aka ce ana yi akan kisan.
Domin tunawa da marigayin iyalai da dangi da abokansa na kut-da-kut sun hallara gidan mahaifiyarsa don yi masa addu’oi.
Shekara 22 bayan kisan General Ba'aré har yanzu dangi na jiran jin yadda abin ya faru don a san wadanda ke da hannu.
Marigayi Ibrahim Ba'are Mainassara wanda ya shugabanci Nijar a zamanin jamhuriya ta 4 mutun ne wanda ake yi wa kyakkyawar shaida.
Yunkurin zakulo wadanda suka hallaka shugaba Ibrahim Ba'aré Mainassara ya citura a nan cikin gida domin wata ayar doka da ke kunshe a kundin tsarin mulkin kasar Nijar ta yin afuwa ga sojojin da suka yi juyin mulkin Janairu 1996 da na Afrilun 1999.
Dalilin kenan da ya sa makusantansa suka garzaya kotun CEDEAO wacce ta umurci gwamnatin Nijar ta biya iyalinsa diyya.
General Ibrahim Ba’are Mainassara wanda ya hau karagar mulki bayan kifar da shugaba Mahaman Ousman a ranar 27 ga watan Janairu 1996 ya shirya zaben da ya ba shi damar doke abokan karawarsa.
Sai 'Yan adawa sun ki amincewa, domin a tunaninsu an yi aringizon kuri’u mafarin barkewar hayaniyar da ta yi sanadin hallaka shi da sunan juyin mulkin wanda Commandant Daouda Malan Wanke ya jagoranta.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5