Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ko Bazoum Zai Iya Magance Rikicin Siyasar Nijar?


Bazoum Mohamed, sabon shugaban kasar Jamhuriyar Nijar.
Bazoum Mohamed, sabon shugaban kasar Jamhuriyar Nijar.

Yayin da aka rantsar da Bazoum Mohamed a matsayin sabon shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, masu lura da al’amuran siyasa na ganin akwai wani babban kalubale, baya ga na hare-haren 'yan ta'adda da na tattalin arziki da ke gabansa – sabon rikicin siyasar kasar da zaben ya haifar.

A lokacin yakin neman zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar, matsaloli biyu da suka fitowa karara, wadanda ‘yan takara suka yi ta shelar za su shawo kansu su ne, matsalar tsaro da ta tattalin arziki da ke addabar kasar.

Nijar na fama da hare-haren mayaka masu ikrarin jihadi akan iyakokinta da Najeriya, Mali da kuma Burkina Faso.

Mutum sama da 200 aka kashe tsakanin watan Janairu zuwa Maris a wani kiyasi da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a watan Maris.

Sannan kasar na gaba-gaba a jerin kasashen da ke fama da matsanancin talauci a duniya a cewar hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP.

Mahamane Ousmane: Tsohon Shugaban Kasar Nijar
Mahamane Ousmane: Tsohon Shugaban Kasar Nijar

Kusan dukkan ‘yan takara 30 da suka nemi wannan kujera ta shugaban kasa, kan wadannan batutuwa biyu suka fi mayar da hankali wajen tallata kansu ga masu kada kuri’a.

Ko da yake, ‘yan takarar sun kuma dora kamfen dinsu akan wasu al’amura da suka shafi kiwon lafiya, ilimi da muhalli.

Masana da dama sun yi ittifakin cewa, Nijar, ba kasa ba ce da ke yawan samun rikicin siyasa – kafin zabe, a lokacin zabe ko bayan zaben.

Shirin Sulhunta Bangarorin Siyasar Nijar 2
Shirin Sulhunta Bangarorin Siyasar Nijar 2

Hasali ma, yakin neman zabe da aka yi na baya-bayan nan, an yi shi lami lafiya, sai dai dan abin da ba a rasa ba, misali na zafafan kalamai da ‘yan takara da magoya bayansu suka rika jefawa juna - abin da mutane da dama suka yi tsammanin zai gushe da zarar kakar zabe ta wuce.

Amma ga dukkan alamu, zaben 2021, ya bar baya da kura, domin tun a zagayen farko da aka yi a ranar 27 ga watan Disambar bara, bangaren ‘yan adawa ya fara cewa an tafka magudi, ikrarin da jam’iyya mai mulki ta PNDS ta musanta.

Dan takarar PNDS, Bazoum Mohamed ya samu kashi 39.30 yayin da babban dan takarar bangaren hamayya Mahamane Ousmane na jam’iyyar RDR ya samu kashi 16.99.

Alkalan kotun tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar
Alkalan kotun tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar

Kundin tsarin mulkin Nijar ya tanadi cewa sai dan takara ya samu kashi 50 da kuri’a daya kafin ya zama shugaban kasa. Hakan ya sa aka tafi zagaye na biyu.

A ranar 21 ga watan Fabrairu al’umar ta Nijar ta sake zabe a zagaye na biyu, wanda Bazoum, mai shekara 60 ya lashe da kashi 55.66 yayin da Ousmane, Wanda tsohon shugaban kasa ne mai shekara 71 ya samu kashi 44.34.

Jim kadan bayan fitar da sakamakon zaben, ya barke a birnin Yamai da wasu sassan kasar.

Hotunan zanga zangar da aka gudanar a birnin Yamai na Nijar, bayan hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.
Hotunan zanga zangar da aka gudanar a birnin Yamai na Nijar, bayan hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.

An kwashe kwanaki akalla uku kafin jami’an tsaro su shawo kan zanga-zangar da ta barke, lamarin da ya kai ga damke wasu daga cikin ‘yan siyasar da gwamnati ta ce su suka tunzura mutane, ciki har da Hama Amadou, babban jagoran bangaren ‘yan adawa.

“Alkaluman da muka tattara sun nuna cewa mu ne muka lashe zabe, saboda haka ina kira ga jama’a da su fito su yi tattaki na lumana don nuna rashin amincewarsu.” Ousmane ya umurci magoya bayansa a farkon makon nan.

Sai da kakakin jam’iyya mai mulki Asoumana Amadou, ya kore ikrarin na Ousmane, yana mai cewa zargin ba shi da tushe balle makama.

An Fara Rigistar Zabe A Wasu Jihohi A Jamhuriyyar Nijer
An Fara Rigistar Zabe A Wasu Jihohi A Jamhuriyyar Nijer

“Shi da kansa Mahamane Ousmane ya san ya sha kasa, duniya gaba daya ta yi shaidan cewa wadannan zabubbuka an yi su tsakani da Allah.” In ji Amadou.

Tun gabanin zaben, an yi ta yayata cewa, idan har aka mika mulki cikin ruwan sanyi a wannan karo, zai zamanto karo na farko da za a yi sauyin gwamnati daga zababbiyar gwamnatin farar zuwa wata.

Kwatsam, a ranar 31 ga watan Maris, sai aka ji harbe-harben bindiga a fadar shugaban kasar da ke Yamai, lamarin da hukumomin kasar suka ce juyin mulki aka yi yunkurin yi, ammam ba a yi nasara ba.

“A daren 30-31 na watan Maris 2021, mun murkushe wani yunkurin juyin mulki. Ana nan ana gudanar da bincike, don gano wadanda ke da hannu a ciki don a kama su, da su da masu goyon bayansu.” Kakakin gwamnati Abdourahmane Zakaria ya fadawa manema labarai a ranar Laraba.

Sojojin Kasar Nijar
Sojojin Kasar Nijar

Kasashen duniya da dama dai sun yi ta Allah wadai da wannan yunkurin juyin mulki wanda bai yi nasara ba.

Masu sharhi dai na ganin ga dukkan alamu, kalubalen da ke gaban Bazoum sun dara na tsaro daga mayakan masu ikrarin jihadi da na tattalin arziki.

A irin kiyasin da jama’a ke yi, babu babban kalubale da ya dara na dinke barakar da aka samu a fagen siyasar wacce ta kunno kai bayan wannan zabe.

Wasu sun yi hasashen cewa mai yiwuwa wata hanya daya tilo da za a iya nemo bakin zaren wannan rikici, ita ce, ta yadda Bazoum zai yi rabon mukamai idan ya zo kafa gwamnati.

Tun bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, Bazoum, ya yi kira ga bangaren na adawa da su zo a hada hannu don a ciyar da kasar ta Nijar gaba, kiran da ‘yan hamayyar suka yi wasti da shi.

XS
SM
MD
LG