An Zargi Shiekh El-Zakzaky Da Laifin Kisan Kai

Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da karar tuhumar shugaban kungiyar Shi’a na kasa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da laifin kisan kai.

Wannan tuhuma da ake yiwa El-zakzaky na da alaka da lokacin da almajiransa suka tare hanya ga kwambar motocin babban hafsan sojin ‘kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Buratai.

An sami wannan labarin ne ta bakin lauyan kungiyar Femi Falana, kuma an shigar da karan tun ranar 17 ga watan nan. Wannan tuhuma idan ta tabbata tana dauke da hukuncin kisa ne.

‘Yan kungiyar Shi’a sun dage da zanga-zangar neman a saki shugaban na su, dake hannun jami’an tsaro tun shekarar 2015.

Da yake mayar da martani kakakin kungiyar Shi’a, Ibrahim Musa, ya ce hakan wata hanya ce ta ci gaba da tsare El-zakzaky, ganin cewa ‘yan kungiyar aka kashe kuma yanzu an dawo ana cewa sune suka yi kisan.

Kakakin kungiyar ya nuna yakinin cewa babu wata hujja da gwamnati za ta iya gabatarwa da zata kai ga samun nasara gaban kotu.

A baya dai gwamntin Najeriya ta ce tana tsare da mallam El-zakzaky ne domin kare lafiyarsa, ba wai hana shi ‘yanci bane, kuma yana tare da uwargidansa domin ta kyautata masa.

Cikin wani faifan sauti anji El-zakzaky daga inda ake rike da shi yana ta’aziyyar ga iyalin daya daga cikin wadanda suka rasa ransu a zanga-zangar ‘yan Shi’ar da ta zayyana cewa zalunci ne.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

An Zargi Shiekh El-Zakzaky Da Laifin Kisan Kai - 2'59"