Shugaban Najeriya Muhammad Buhari na fuskantar barazanar tsigewa yayinda majalisaun dokokin kasar suka gano cewa ya kashe wasu kudade kimanin dalar Amurka miliyan 496 ba tare da amincewarsu ba.
Shugaban ya yi anfani da kudaden ne wajen sayen wasu jiragen sama na yaki daga Amurka da za'a yi anfani dasu a inganta tsaro.
Wani Sanata Matthew Iregede dan jam'iyyar PDP daga jihar Edo shi ya jawo hankalin majalisar dattawa akan dokar da ta ce idan gwamnati zata kashe kudi masu yawa haka wajibi ne ta nemi amincewar majalisun. A cewarsa shugaban kasa bai yi hakan ba akan sayen jiragen.
'Yan majalisar dattawa sun dauki lokaci mai tsawo suna muhawara akan batun da Iregede ya kawo. Amma daga bisani shugaban majalisar Dr. Bukola Saraki ya bada shawarar a mika batun ga kwamitin kula da harkar shari'a ya yi bincike ko shugaban ya sabawa kundun tsarin mulkin kasa. Abu na biyu kuma kwamitin ya duba ko yanayin da ake ciki ya tanadi shugaban ya aikata abun da ya yi.
Onarebul Inusa Ahmed Abubakar dan jam'iyyar APC daga jihar Gombe yana da ra'ayin cewa 'yan adawa ne ke tada hankalin mutane a majalisun biyu. Shugaban ba ya sace kudin ba ne. Baicin hakan ya amince da sayen jiragen saboda halin da ake ciki kuma ya kira majalisun su gyara abun da gwamnati ta yi.
Shi ma Ahmed Babba Kaita dan jam'iyyar APC daga jihar Katsina ya ce ba'a Najeriya kadai shugaba ke daukan irin matakin ba, musamman idan harkar tsaro ta taso.
Ga Medina Dauda da karin bayani a wannan rahoton
Facebook Forum