Shawarar Da Amurka Ta Ba Netanyahu Kan Yadda Za A Kawo Karshen Yakin Gaza

Blinken, (Hagu) yayin ziyarar da ya kai Gabas ta Tsakiya

Netanyahu, kamar yadda rahotanni suka nuna a ganawar ta tsawon sa’o’i biyu da rabi, ya shaida wa Blinken cewa kisan Sinwar zai iya kawo “kyakkyawan tasiri” wajen sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma cimma burin Isra’ila na kawo karshen mulkin Hamas.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, a ranar Talata ya yi kira ga Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da ya yi amfani da kisan da aka yi wa jagoran Hamas Yahya Sinwar makon da ya gabata domin kawo karshen yakin da ke gudana tsakaninsu da Hamas a Gaza, da kuma tabbatar da sakin ragowar mutanen da aka yi garkuwa da su 101, wadanda daga cikinsu ana tsammanin kimanin 60 na nan da rai.

Netanyahu, kamar yadda rahotanni suka nuna a ganawar ta tsawon sa’o’i biyu da rabi, ya shaida wa Blinken cewa kisan Sinwar zai iya kawo “kyakkyawan tasiri” wajen sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma cimma burin Isra’ila na kawo karshen mulkin Hamas a wannan yanki da ke bakin teku na Bahar Rum.

Babban jami’in diflpmasiyyar na Amurka, wanda wannan shi ne ziyararsa ta 11 zuwa Gabas ta Tsakiya tun bayan barkewar yakin Isra’ila da Hamas fiye da shekara guda da ta wuce, ya kuma matsa wa Netanyahu lamba ya bari a kara kai agajin jin-kai ga mutanen Falasdinawa da ke fama da yunwa a Gaza, musamman daruruwan fararen hula da yakin ya rutsa da su a arewacin Gaza da ke da wahalar kai wa.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Matthew Miller, ya ce Blinken ya yi kira ga shugaban na Isra’ila da ya kawo karshen “rikicin da ke Gaza ta yadda za a samu cikakken tsaro mai dorewa ga Isra’ilawa da Falasdinawa baki daya.”

Ya kuma tattauna muhimmancin bullo da sabon tsarin ci gaba bayan rikicin wanda zai bai wa Falasdinawa damar farfado da rayuwarsu, tare da tabbatar da mulki, tsaro, da sake gina Gaza, in ji Miller.

Netanyahu da Blinken sun kuma tattauna game da ci gaba da yakin Isra’ila da mayakan Hezbollah da Iran ke mara wa baya da ke Lebanon.