Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Barazanar Janye Tallafin Kayan Sojin Da Take Ba Isra’ila


Shugaban Amurka, Joe Biden
Shugaban Amurka, Joe Biden

Kalaman na Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke kai hari kan mayakan Hezbollah a Lebanon da sabunta hare-haren da take kai wa kan Hamas a arewacin Gaza.

Amurka ta bukaci Isra’ila da ta kara fadada ayyukan jin-kai ga Fasladinawa da ke fama da yunwa a Gaza a cikin wata mai zuwa ko kuma ta fuskanci yiwuwar katse taimakon soji da take bai wa Isra’ila a yakin da ta shafe shekara guda tana yi da mayakan kungiyar Hamas.

Gargadin ya zo ne a ranar Lahadin da ta gabata a wata wasika da Washington ta aike wa jami’an Isra’ila tare da nuna matukar damuwa kan tabarbarewar ayyukan jin-kai a Gaza.

“Abin da muka gani a cikin ‘yan watannin da suka gabata shi ne, yanayin ayyukan jin-kai ba ya dorewa. A gaskiya, sun yi kasa da sama da kashi 50 cikin 100 daga inda yake a kololuwarsa a baya.” In ji Matthew Miller, Kakaki a Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.

Kalaman na Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hari kan mayakan Hezbollah a Lebanon da sabunta hare-haren da take kai wa kan Hamas a arewacin Gaza.

Tsawon watanni, duk da cewa fadan Isra’ila da Hamas na ci gaba, Amurka ta sha matsawa Isra’ila lamba da ta kara bari a shigar da kayayyakin agajin jin-kai cikin yankin, wadanda suka hada da abinci, ruwa, magunguna, man fetur da sauran kayayyaki zuwa ga fararen hula Falasdinawa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG