Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra’ila Tace Wani Harin Jirgi Mara Matuki Ya Kaikaici Gidan Priminista Benjamin Netanyahu


Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu
Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu

Gwamnatin Isra’ila tace, wani jirgi mara matuki ya kaikaici gidan priminista Benjamin Netanyahu a ranar Asabar, ba tare da wani ya jikkata ba, yayin da babu wata alama tayin sanya a fadan da ake cigaba da gwabzawa da mayakan Hezbollah a Lebanon, da na Hamas dake Gaza, duk kuwa da kisan wanda ya kitsa harin na ranar 7 ga watan Oktoba.

Sojojin Isra’ila sunce, an kaddamar da gwamman hare hare daga Lebanon, kwana guda bayan Hezbollah ta sanar da bude wani sabon babi a fadan. Ofishin Netanyahu yace, harin jirgi mara matukin ya kaikaici gidan sa ne dake garin Caesarea dake yankin gabar ruwan mediterreniya. Daga shi har matar shi dai basa cikin gidan a lokacin, babu kuma tabbacin ko harin ya samu gidan.

Netanyahu yace, ‘a yau yan koren Iran da sukayi kokarin hallakani da mai dakina sun tabka mummunan kuskure’.

Hezbollah dai bata dauki alhakin harin jirgi mara matukin ba, to sai dai tace, ta kai hare haren rokoki a arewaci da tsakiyar Isra’ila. Harin yazo ne a daidai lokacin da akayi hasashen Isra’ila zata maida martani ga wani hari da Iran ta kai a farkon watan nan, wadda ke marawa Hezbollah da Hamas baya.

A nata bangaren, Isra’ila ta kai akalla hare hare ta sama 10 a kewayen kudancin Beirut da aka sani da Dahiyeh, yanki mai shakare da jama’a inda ofisoshin Hezbollah suke, cewar hukumomin Lebanon. Sojojin Isra’ila sunce sun kai hari kan wuraren Hezbollah.

A can Gaza kuwa, dakarun Isra’ila sun kai hari kan asibitoci a kewayen arewacin Palasdinu da akayi pata pata da shi, haka zalika, hare hare ya kashe mutane sama da 50 da ya hada da kananan yara a cikin kasa da sa’oi 24, cewar jami’an asibiti da wakilin kafar yada labarum Associated Press dake yankin.

‘Har yanzu yuwuwar barkewar yaki a yankin na cigaba da zama abin damuwa matuka’ cewar ministan harkokin wajen kasar Parisa wato Iran Abbas Araghchi, a lokacin da ya ziyarci Turkiyya. Wani ayarin ministocin tsaron su 7 yayi gargadin rincabewar al’amurra da shiga yaki gadan gadan. Tuni dai kashen Amurka, Birtaniya da sauran kasashen yamma suka aiyana Hamas da Hezbollah a matsayin kungiyoyin ta’addanci.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG