Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Isra’ila Ta Kashe Shugaban Hamas Yahya Sinwar


Yahya Sinwar
Yahya Sinwar

Katz ya kwatanta kashe Sinwar a matsayin wata "gagarumar nasara ga sojojin Isra’ila."

Isra'ila ta sanar a ranar Alhamis cewa ta kashe shugaban Hamas, Yahya Sinwar, wanda shi ake zargi da kitsa harin ta'addancin da ya faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023, wanda ya janyo rikicin Gaza.

Rundunar sojojin Isra'ila — wacce babu tsammani ta yi ido hudu da Sinwar ba tare da sanin inda yake ba ta yi karo da shi da wasu mayaka guda biyu a wani gini a kudancin Gaza, sannan suka bude wuta.

Kusan nan take Isra’ila ta yi zargin cewa ta kashe Sinwar, mai shekaru 61, amma sai da ta tabbatar bayan sa'o'i tana bincike kan kwayoyin halittunsa na DNA da bayanan hakoransa.

"Maharin da ya kashe mutane da yawa, Yahya Sinwar, wanda ya ke da alhakin kisan gillar da aka yi a ranar 7 ga Oktoba, an kashe shi yau ta hannun sojojin IDF," in ji Ministan Harkokin Wajen Isra'ila, Israel Katz, cikin wata sanarwa.

Katz ya kwatanta kashe Sinwar "gagarumar nasara ga sojojin Isra’ila."

"Kisan Sinwar zai samar da damar sakin fursunonin nan take da kuma kawo wani sauyi da zai haifar da wani sabon yanayi a Gaza — ba tare da Hamas ba kuma ba tare da ikon Iran ba," in ji shi.

Amma tasirin kisan Sinwar kai tsaye bai tabbata ba. Tattaunawar tsagaita wuta a rikicin Gaza ta tsaya cik na tsawon watanni, inda Hamas da Isra'ila ke kin amincewa da cikakkun bayanai kan duk wani tsagaita wuta.



Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG