'Yan ta'adda sun yi yunkurin samun gindin zama a kasar yayin da rarrabuwar kan siyasa ta bude kofa ga shugabannin yaki da suka raba kasar, inda suke ta fada a kan yankuna da rijiyoyin mai. Kuma a halin da ake ciki, kungiyoyi masu daukar manyan makamai wadanda suka samo asali daga mayakan da aka kafa bayan juyin juya halin 2011, na gudanar da ayyuka a fadin kasar, ba tare da an taka musu burki ba.
"Amurka ta damu matuka a kan ayyukan kungiyoyin mayaka a Libya, da ke cin karensu babu babbaka ba tare da an hukunta su ba, kuma suna tasiri kan tsaro da siyasar Libya," in ji Robert Wood, jakadan Amurka a bangaren Harkokin Siyasa na musamman a Majalisar Dinkin Duniya.
“Har yanzu muna da damuwa kan yawan take hakkokin dan Adam da dokokin jin kai na kasa da kasa da wadannan kungiyoyi ke yi, abin da ya hada da kisa, raunatawa, ko kuma raba daruruwan fararen hula da muhallansu; da kuma zarge-zargen tsare mutane ba bisa ka'ida ba. Muna kira ga kwamitin da ya ci gaba da gudanar da bincike kan wadannan ayyukan tare da gano mutanen da ta yiwu a sanya masu takunkumai."
Tattalin arzikin Libya ya dogara sosai kan man da take fitarwa zuwa kasashen waje. Hakika, man fetur shi ke samar da kudin shiga sama da kashi 90 cikin 100 a shekara. Sai dai duk da haka ba a rarraba kudaden daidai a yankuna uku na Libya, wato Tripolitania, Cyrenaica da Fezzan.
"Muna ci gaba da kira ga shugabannin Libya da su himmatu wajen aiwatar da tsarin gaskiya, adalci don kula da rarraba kudaden shigar da ake samu na mai," in ji jakada Wood.
A karshe, a bayyane yake babu wata hanya ta samar da makomar zaman lafiya a kasar Libiya ba tare da zabe ba.
"Muna kira ga shugabannin siyasar Libya da su zabi wakilansu da zasu halarci zaman sharar fage da Majalisar Dinkin Duniya zata taimaka a yi, da nufin magance muhimman batutuwan da ke hana gudanar da zabe," a cewar jakada Wood.
"Za a dora laifin sosai kan wadanda ke ci gaba da kawo jinkiri a shirin zaben idan aka ci gaba da bata lokaci ba tare da yin zaben halaltacciyar gwamnati ba."
Al'ummar Libya sun cancanci canji, ci gaba, da fata na gari. Sun kuma cancanci su zabi shugabanninsu.