SHARHIN AMURKA: Wajibi Ne Kwamitin Tsaro Na MDD Ya Hukunta 'Yan Tawayen Houthi Da Kasar Iran

Jakada Dorothy Shea a lokacin wata tattaunawa da shugaban kasar Lebanon 2022

Bayan shafe shekara guda suna kaiwa Isra'ila hari da makamai masu linzami, 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran sun zafafa hare-haren da suke kaiwa a makonnin baya-bayan nan

Dimbin hare-haren da 'yan tawayen Houthi suka kai a watan Disamban da ya gabata sun hada da harin da aka kai kan wata makarantar firamare dake tsakiyar Isra'ila da kuma wanda ya fada kan wata unguwar zaman jama'a a Jaffa, wanda ya jikkata akalla farar hula 16. Haka kuma, 'yan Houthi sun ci gaba da kaiwa jiragen ruwan kasuwanci hari a tekun bahar ahmar.

A yayin wani taron kwamitin tsaron MDD, mataimakiyar wakiliyar Amurka a majalisar, Dorothy Shea ta sake jaddada kiran da kasar ta yiwa kwamitin tsaron na duba yiyuwar daukar karin matakan yin martani ga karuwar barazanar dake fitowa 'yan Houthi tare da hukunta kasar Iran.

"Dukkaninmu na iya gani karara cewa Iran ta karfafa 'yan tawayen Houthi a kan yadda za su iya kaddamar da munanan hare-hare a kan Isra'ila da makamai masu cin dogon zango, ciki har da kayayyakin more rayuwar farar hula, kamar yadda ta bayyana a farfagandar cika bakin da 'yan houthi ke yi a kan yin amfani da makamai ma su linzami na zamani masu gudun tsiya.

Samarwa 'yan Houthi da wadannan da sauran miyagun makamai ya sabawa takunkumin da wannan kwamitin ya kakabawa kungiyar."

Jakada Shea ta jaddada cewa hakkin kwamitin tsaron ne ya mayar da martani akan sabawa kudurorinta da kuma samawa kungiyoyin 'yan ta'adda makamai.

"Kowane mamba na wannan kwamitin-musammanma wadanda keda alaka ta kai tsaye da Iran-kamata yayi su yiwa shugabaninta matsin lamba a kan su hana 'yan Houthi kaddamar da hare-hare daka iya jefa farar hula cikin hatsari."

Haka kuma, Jakada Shea ta ce, kamata yayi kwamitin tsaron ya karfafa tsarin tantancewa da sanya idanun MDD (UVIM), da ke kula da harkokin kasuwanci da taimakawa yarjejeniyar kasa da kasa a kan kayan da za su isa kasar Yemen.

Abu mai mahimmanci, shi ne UVIM na neman tabbatar da cewar Iran da kawayenta sun daina samawa 'yan Houthi makamai bisa sabawa takunkumin hana hakan

Haka kuma Jakada Shea ta ce tana goyon bayan tsawaita bukatar rahoton kwamitin tsaron dake kunshe cikin kuduri na 2722, wanda ya bukaci babban sakataren MDD ya rika ba da rahoton wata-wata game da hare-haren 'yan Houthi a kan jiragen ruwan kasuwanci.

Ta jaddada cewa hare-haren baya-bayan nan da Amurka ta kaiwa wuraren da Houthi ke amfani dasu wajen kai hari kan jiragen ruwan soja dana kasuwancin Amurka "sun dace da dokokin kasa da kasa da kuma damar Amurka na kare kanta."

Jakada Shea ta ayyana cewa, "lokaci ya yi da 'yan Houthi za su dakatar da dabi'arsu ta ganganci da tarwatsa al'amura kuma kamata yayi wannan kwamitin ya tabbatar da cewa sun girbi abin da suka shuka."

Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.