“Saboda sanin cewa duniyar da ake mutunta hakkokin bil adama ta dace da muradanmu. Shekaru 4 da suka gabata sun kara fayyace cewa, a bisa babban mizani, kasashen da ake mutunta hakkin dan adam sun fi samun daidaito da tsaro da zaman lafiya. Su fi zama kawaye ababen dogaro. Sun fi zama sahihan hadimai a duniyar da muke tarayya a ciki.”
Masu karbar kyautar kiyaye hakkin dan adam ta bana mutane masu karfin hali wadanda ke burin shiga kowane irin hatsari domin kare hakkokin bil adama.
Daya daga cikinsu ita ce Juana Alicia Ruiz. Bayan yakin basasar Columbia, ta shiga sahun matan yankin wajen kirkirar ayyukan da za su taimakawa mutanen da suka tsira da rayukansu su tuna irin cin zarafin da suka fuskanta tare da kwantar da hankulansu ta hanyar rarrashi.
A kasar Ghana, Ebenezer Peegah da kungiyarsa sun soma samarwa tare da rarraba bayanai ta yanar gizo da zasu rika taimakawa ‘yan luwadi da madigo da bayanan da suke bukata domin kaucewa kungiyoyin sintiri.
Mary Ann ta bar gidanta a kasar Phillipines zuwa Kuwait inda ta kare a matsayin ‘yar aikin gida, inda ta jurewa ci da guminta da cin zarafi. Ta hada kai da takwarorinta ma’aikata wajen kirkirar kungiyar fafautukar kare hakkin ‘yan aikin gida da sauran bakin hauren dake leburanci a Kuwait.
A kasar Arzerbaijan, an zargi Rufat Safarov da laifin bada cin hancin bogi tare da tura shi zuwa gidan kaso tsawon shekaru 9 a bisa shari’ar rashin adalci. Bayan sakinsa, ya kafa kungiyar taimakawa wajen kare hakkokin mutanen da ake kaiwa hari saboda kare hakkin dan adam. Gwamnatin kasar ta sake tsare shi saboda ya nemi iznin zuwa Amurka, a cewar Sakatare Blinken.
“Ya kamata gwamnatin Arzerbaijan ta saki Rufat-kuma ta gaggauta sakin nasa-tare da sauran ‘yan jaridu, da masu kare hakkin dan adam, da ‘yan adawar siyasa da sauran mutanen da ake tsare dasu ba bisa adalci ba.”
Thulani Rudolph Maseko ya sadaukar da ilahirin rayuwarsa wajen dabbakar akidar kare hakkin dan adam a Eswatini. A ranar 21 ga watan Jamairun 2023, aka harbe tare da hallaka shi a gidansa. Har yanzu babu wanda aka kama akan hakan.
Sauran wadanda suka samu wanna karramawa harda aida Dzhumanazarova daga Kyrgyzstan da Mang Hre Lian daga Burma da Ampero Carvajal na Bolivia.
“( Ga wadanda za’a karrama a yau,” a cewar Sakatare Blinken: ga dukkanin masu yaki akan kare hakkin dan adam a fadin duniya: ina buktarku ku cigaba da nuna misali. ku cigaba da kalubalantarmu wajen tabbatar da kwarin giwarku. Ku cigaba da bin diddiginmu.”
Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.
Dandalin Mu Tattauna