SENEGAL: Magoya Bayan Sanko Sun Yi Arangama Da ‘Yan Sanda Bayan Yanke Mashi Hukumcin Dauri

SENEGAL-

Ana zargin Sonko mai shekaru 48 da haihuw, da laifin yiwa wata mata da ke aiki a gidan da ake tausar jiki, fyade a shekarar 2021, tana da shekara 20, da kuma yi mata barazanar kisa. Sonko ya musanta aikata haka, ya kuma ce zargin na da alaka da siyasa ne.

WASHINGTON, D. C. - Magoya bayan Ousmane Sonko madugun 'yan adawar a Senegal sun yi arangama da ‘yan sandan kasar har suka kai ga jefan 'yan sandan kwantar da tarzoma, da kuma kona motocin safa yau Alhamis, sakamakon hukuncin da wata kotu ta yanke wa Ousmane Sonko na daurin shekaru biyu a gidan yari, lamarin da zai iya hana shi tsayawa takarar shugaban kasa a shekara mai zuwa.

Senegal Opposition Leader

Kotun da ke hukunta manyan laifuka ta wanke Sonko daga laifin fyade, amma ta same shi da wani laifi dabam da aka bayyana a cikin kundin tsarin mulkin kasar a matsayin rashin da’a da ya yi wa wasu matasa ‘yan kasa da shekara 21.

Da wannan hukunci, Sonko ba zai iya tsayawa takara ba," in ji daya daga cikin lauyoyinsa, Bamba Ciss, bisa la’akari da dokar zaben Senegal.

Senegal

Jam’iyyar PASTEF ta Sonko ta ce wannan hukunci wata kullalliya ce ta siyasa. Dalilin haka ne Jam’iyyar ta yi kira ga ‘yan kasar baki daya a cikin wata sanarwa da su “dakatar da duk wani aiki don su fito kan tituna su yi zanga-zanga.

Sonko bai halarci zaman kotun ba. Amma duk da haka Alkali mai shari'a Ismaila Madior Fall ya ce daga yanzu ana iya kama Sonko a kai shi gidan yari a kowanne lokaci, kuma an girke 'yan sanda a kusa da gidansa da ke Dakar domin kare lafiyar jama'a.

-Reuters