Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban ‘Yan Adawar Senegal Zai Fuskanci Shari'a Kan Zargin Fyade, Da Barazanar Kisa


Ousmane Sonko, Senegal
Ousmane Sonko, Senegal

Ana zargin shugaban 'yan adawar kasar Senegal, Ousmane Sonko ne da fyade da yin barazanar kisa ga wata ma'aikaciyar salon din kwalliya a shekarar 2021, kamar yadda wani alkali mai bincike ya bayyana a wata wasika.

WASHINGTON, D.C. - Alkalin ya mika batun ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasar Senegal, domin yi masa shari'a a wata wasika mai dauke da kwanan watan 17 ga watan Janairu wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani a ranar Laraba.

Lauyan Sonko bai amsa bukatar jin ta bakinsa ba, sai dai Sonko ya musanta dukkan tuhumar da ake masa.

Shari'ar na iya kawo cikas ga aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2024. ‘Dan siyasar mai shekaru 48, wanda ya zo na uku a zaben 2019, ya bayyana cewa zai tsaya takara.

Hakan na iya haifar da dambarwar siyasa a Senegal. Rikici ya barke a kasar a watan Maris din shekarar 2021 lokacin da alkalin mai binciken ya gayyaci Sonko da farko inda aka kama shi.

Ana zargin Sonko da yin lalata da wata mata da ke aiki a wani wurin tausa, sannan kuma ya yi mata barazana. Shi da masu mara masa baya sun ce shari’ar na da nasaba da siyasa domin kawar da shi daga takarar shugaban kasa.

Yana samun goyon baya sosai a tsakanin matasan kasar Senegal, da dama daga cikin wadanda ke cike da takaicin gwamnati, saboda rashin aikin yi da matsalolin tattalin arziki sun ci gaba da tsanani, lamarin da ke haifar da zanga-zangar, wasu lokutan kuma masu har da tayar da hankali.

El Hadj Diouf, lauyan mai kara ya ce wadda yake karewa ta ji ‘da’din hukuncin da alkalin ya yanke.

"Abin bai zo da mamaki ba, ba mu da wani abu da za mu boye," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho.

Wasu jiga-jigan 'yan adawa da magoya bayan Sonko na fargabar cewa lamarin wani yunkuri ne na shugaban kasar Senegal Macky Sall, mai shekaru 61, na neman tsige wani abokin hamayyarsa idan ya yanke shawarar neman wa'adi na uku, sakamakon raguwar goyon bayansa.

Gwamnatin Sall dai ta yi watsi da zargin tana mai cewa lamarin na kotuna ne.

A baya dai an fuskanci tuhume-tuhume da wasu ‘yan hamayya da suka hada da tsohon magajin garin Dakar Khalifa Sall da Karim Wade dan tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade wanda ya kawar da su daga takarar shugabancin kasar a zaben 2019.

Wa'adin Sall na biyu dai zai kare ne a shekarar 2024. Bai kuma bayyana ko zai tsaya takara karo na uku ba.

-Reuters

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG