SENEGAL: An Ayyana Zaman Makokin Kwanaki Uku Bayan Mummunan Hadarin Mota

died and scores were injured when two buses collided.

Akalla mutane 40 ne suka mutu inda wasu 87 suka jikkata bayan da wasu motocin bas guda biyu suka yi karo a kusa da Kaffrine a tsakiyar kasar Senegal.

WASHINGTON, D.C. - Hadarin ya afku ne a kan babban titin kasar da misalin karfe 3:15 na safiyar Lahadi.

Shugaba Macky Sall ya ce mutane 40 ne suka mutu a mummunan hatsarin kuma ya sanar da kwanaki uku na zaman makoki a kasar.

Shugaban kasar Senegal Macky Sall, Sept. 20, 2022.

Babbar motar Bas din mai kujeru 60 ta na kan hanyar zuwa Rosso kusa da kan iyaka da Mauritania ne, hukumar kashe gobara ta ce ba a san adadin mutanen da ke cikinta ba.

Shugaban ayyuka na hukumar kashe gobara ta kasa Kanal Cheikh Fall, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, "Hatsari ne mai tsanani," ya kara da cewa mutane 87 ne suka jikkata a lamarin.

An kai wadanda abin ya shafa asibiti da cibiyar kula da lafiya a Kaffrine, in ji shi. Fall ya kuma ce, an kawar da baraguzan motocin bas din kuma a yanzu haka ana ci gaba da zirga-zirga da ababen hawa akan hanyoyin.

-AFP