Jami’ar yada labarai ta kungiyar Agaji ta Red Cross a kasar, Irene Nakasiita, ta fada yau Laraba cewa hadarin ya faru ne a kan babbar hanyar Fort Portal-Kasese, wata hanya mara fadi da ake aikin shimfida ta a gundumar Kasese.
Rahotannin farko sun nuna cewa wata babbar mota da ke tsala gudu dauke da akwatin gawa ta yi karo da wata motar, kafin mota ta uku dake dauke da mutane da dama ta kwace, kana su kuma sauran direbobin biyu suka rasa yadda za su yi, suka buga wa motocin da suka lalace.
Jaridar Daily Monitor ta Uganda ta zanta da wani da ya shaida lamarin wanda ya ce karo da motocin farko suka yi, shi ya janyo sauran haduran.
‘Yan sanda na nan suna kokarin tantance musabbabin hadura a Uganda, inda hatsiran mota ke hallaka sama da mutu dubu biyu a kowacce shekara, lamarin da ya saka kasar a cikin jerin kasashen da hatsiran ababen hawa ke lakume rayuka.